Rashin takunkumin fuska: Yadda aka hana masu sallah shiga masallacin Juma'a a Jos

Rashin takunkumin fuska: Yadda aka hana masu sallah shiga masallacin Juma'a a Jos

- An hana wasu masallata shiga masallacin Juma'a a Jos don bin jam'i saboda rashin sanya takunkumin fuska

- Sai dai an bari wadanda suka saka takunkumin fuska sun shiga masallacin inda wadanda basu saka ba suka yi a waje

- An kuma bar tazara a tsakanin masallatan a yayin da ake sallar Juma'ar

A ranar Juma'a ne aka hana masu salla shiga babban masallacin Juma'a na Jos don yin sallar jam'i sakamakon kin saka takunkumin fuska da suka yi.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, an bar masu bauta da suka saka takunkumin fuska shiga masallacin amma na bar marasa takunkumin fuska a waje don yi sallah.

Hakazalika, akwai tazarar da ta dace tsakanin masallatan a yayin da ake sallar Juma'a.

A ranar Alhamis ne masallacin ya bayyana dokokin zuwa sallar Juma'a. Matakan sun hada da amfani da takunkumin fuska ga dukkan wadanda ke son yin sallah a cikin masallaci.

Rashin takunkumin fuska: Yadda aka hana masu sallah shiga masallacin Juma'a a Jos
Rashin takunkumin fuska: Yadda aka hana masu sallah shiga masallacin Juma'a a Jos Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Wannan ce sallar Juma'a ta farko da aka yi a jihar Filato tun daga watan Afirilu da gwamnatin jihar ta bada umarnin rufe dukkan wuraren bauta na jihar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa za ta sake shawara a kan matakin da ta cimma na bude wuraren ibada a kasar idan har ba a bin sharuddan da ta gindaya.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da korona na shugaban kasa, PTF, Boss Mustapha, a yayin jawabin kwamitin a ranar Alhamis ya ce an raba wa jihohi sharrudan.

Ya ce gwamnatin tarayya na sa ran shugabanin addinai za su amince da sharrudan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce akwai bukatar jihohin su dage wurin wayar da kan mutane game da cutar don hana tsangwama da kawar da canfe canfe, inda ya kara da cewa sarakuna da shugabannin addinai suna da rawar da ya dace su taka.

Mustapha ya shawarci yan Najeriya game da hatsarin da ke tattare da shan magunguna ba tare da tuntubar likitoci ba duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta cigaba da gwajin da ta ke yi na hydroxychloroquine.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel