Yanzu-yanzu: Saudiyya za ta mayar da dokar kulle, ta bada sharudda 4

Yanzu-yanzu: Saudiyya za ta mayar da dokar kulle, ta bada sharudda 4

Ma'aikatar cikin gida ta kasar Saudiyya ta bayyana shirinta na dawo da dokar hana zirga-zirga a garin Jeddah na kwanaki 15, wanda zai fara a ranar Asabar, 6 ga watan Yunin 2020.

Idan za mu tuna, masarautar ta bayyana raguwar masu cutar korona amma kuma sai akasin haka ya faru a kwanaki biyu da suka gabata.

A ranar Alhamis, an samu karin mutum 1,975 masu cutar korona, kwanaki hudu bayan sassauta dokar hana zirga-zirga da kuma bude manya da kananan masallatai da ke fadin masarautar.

A ranar Juma'a, Saudi Gazette ta ruwaito cewa ma'aikatar lafiya ta kasar ta bayyana ci gaba da yaduwar cutar amma mutum 806 ne suka warke a ranar.

Yanzu-yanzu: Saudiyya za ta mayar da dokar kulle, ta bada sharudda 4
Yanzu-yanzu: Saudiyya za ta mayar da dokar kulle, ta bada sharudda 4 Hoto: Reuters
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Daga cikin sabbin masu cutar, an samu mutum har 675 a birnin Riyadh, a Makkah an samu 286, a Jeddah an samu karin mutum 259, a Madinah an samu karin mutum 124 sai kuma Hufof an samu karin mutum 112.

Jimillar masu cutar a masarautar a halin yanzu sun kai 93,157 amma mutum 68,965 ne suka warke.

Kamar yadda rahoton Saudi Gazette ya bayyana, sabbin matakan da za a dauka sun hada da

1. Hana walwala daga karfe 3:00 na rana zuwa 6:00 na safe.

2. Dakatar da sallar jam'i tare da rufe masallatai.

3. Dakatar da ma'aikatan gwamnati, ma'aikatu, cibiyoyi da masu zaman kansu.

4. Dakatar da bude dukkan gidajen abinci tare da hana taron fiye da mutum 5.

Amma kuma, za a bar jama'a su yi walwala a cikin sa'o'in da ba na dokar ba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Zikrullah Kunle Hassan, shugaban hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON), ya ce mai yiwuwa kasar Saudiyya ta dakatar da wasu kasashe daga halartar aikin Hajjin bana.

Idan hakan ta tabbata, kasashen da hukuncin zai shafa sune wadanda aka samu tsanantar annobar cutar korona.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taro mai taken "makomar aikin Hajj da Umrah bayan annoba", wanda kungiyar masu ruwa da tsaki a aikin Hajji da Umrah a Najeriya suka shirya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel