'Yan fashi sun kashe 'yan sanda takwas, sun yi sata a banki a Kogi

'Yan fashi sun kashe 'yan sanda takwas, sun yi sata a banki a Kogi

Wasu gungun 'yan fashi da makami sun kashe jami'an rundunar 'yan sanda takwas da su ka hada da DPO tare da yin fashi a wani tsohon banki a garin Isanlu da ke karamar hukumar Yagba ta Gabas a jihar Kogi.

A wani takaitaccen sako da gidan talabijin na TVC ya wallafa, ya ce an kai harin ne da tsakar ranar Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa babu isassun bayanai dangane da harin da 'yan bindigar su ka kai har ya zuwa yammacin ranar Alhamis da ta wallafa labarin.

Kakakin rundunar 'yan sanda (PPRO), DSP William Ayah, ya ce sun kasa zamun DPO ko wani jami'in dan sanda da ke ofishin Isanlu a wayar salula, lamarin da ya sa mataimakin kwamishina mai kula da atisaye ya tafi garin.

Ya kara da cewa mataimakin kwamishinan ya tafi Isanlu ne domin kai dauki ga 'yan sandan ofishin garin Isanlu da kuma ganewa idonsa abinda ya ke faruwa bayan samun rahoton kai harin.

DUBA WANNAN: An kama matashi dan 25 ya na yi wa dattijuwa 'yar 85 fyade a karamar hukumar Rafi

Da ya ke magana da Daily Trust ta wayar tarho, DSP Ayah ya ce, "farar hula sun sanar da mu cewa an kai hari banki da ofishin 'yan sanda a Isanlu, ba zan iya baku karin bayani ba saboda har yanzu ba mu samu damar yin magana da DPO ko wani dan sanda a ofishin garin ba."

Sai dai, wata majiya ta ce 'yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda na Isanlu tare da kashe dukkan jami'an 'yan sandan ofishin kafin daga bisani su yi awon gaba da makamai daga ofishin.

Majiyar ta ce 'yan bindigar kusan su bakwai sun isa bankin a cikin motoci biyu inda su ka hallaka mutane da yawa.

A cewar majiyar, 'yan bindigar sun kashe maigadin da ke tsaye a bakin kofar shiga bankin kafin daga bisani su shiga harabar banki, inda su ka kase kwastomomi da ma'aikatan bankin.

Majiyar ta ce 'yan bindigar sun shafe kusan sa'a guda su na cin karensu babu babbaka kafin daga bisani su bar harabar bankin a motocinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel