COVID-19: Dan majalisa da karin mutum 3 sun rasu a Nasarawa

COVID-19: Dan majalisa da karin mutum 3 sun rasu a Nasarawa

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, ya tabbatar da mutuwar mutum hudu cif a jihar sakamakon annobar korona.

Gwamnan ya bada wannan sanarwar ne a lafiya yayin taro da kwamitin yaki da cutar na jihar ta gudanar.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, cike da alhini yake sanar da mutuwar mutum hudu wanda suka hada da dan majalisar jihar mai wakiltar Nasarawa ta yamma daga cikin mutum 90 da suka kamu da cutar coronavirus a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa, samfur 705 aka kai wa hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya tun bayan da aka fara gwajin.

COVID-19: Dan majalisa da karin mutum 3 sun rasu a Nasarawa
COVID-19: Dan majalisa da karin mutum 3 sun rasu a Nasarawa Hoto: The Sun
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Daga cikin samfur 705 da aka kai mun samu sakamakon 658 amma 90 daga cikin ne suka bayyana dauke da cutar yayin da sauran suke lafiya kalau.

"Wadanda ke karbar maganin cutar a cibiyoyin killacewa na fadin jihar nan na samun sauki," Sule ya kara da cewa.

Gwamnan ya tabbatar wa da jama'ar jihar cewa gwamnatinsa za ta bai wa walwala, lafiya da tsaro fifiko, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya mika godiyarsa ga sarakunan gargajiya, jami'an tsaro, masana kiwon lafiya, manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki a kan yadda suka bashi hadin kai wurin yakar cutar.

Sule ya mika godiyarsa ga Allah da yasa shugaban kungiyar kiristoci ta jihar Joseph Masin, ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane.

KU KARANTA KUMA: Edo 2020: Obaseki zai yi nasara a kowanne irin zaben fidda gwani da za a yi - Shaibu

Ya mika godiyarsa ga cibiyoyin tsaro tare da iyalansa a kan namjin kokarin da suka yi bayan da aka yi garkuwa da shugaban.

A baya mun kawo maku cewa Miracle, dan Joseph Masin, shugaban kungiyar kiristoci ta kasa reshen jihar Nasarawa, ya ce iyalansa sun siyar da motoci uku kafin biyan kudin fansa don sakin mahaifinsu.

An yi garkuwa da Masin a ranar 28 ga watan Mayu yayin da 'yan bindiga suka kutsa gidansa wurin karfe 11 zuwa 12 na dare. Bayan kwanaki uku kuwa an sako shi daga hannun masu garkuwa da mutanen.

A wata tattaunawar da The Punch ta yi da Miracle, ya ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci naira miliyan 50. Sun siyar da motoci uku don samun kudin fansar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng