Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa shugabannin tsaro kiran gaggawa

Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa shugabannin tsaro kiran gaggawa

Majalisar wakilai ta yanke hukuncin yi wa shugabannin tsaro kiran gaggawa sakamakon hauhawar rashin tsaro a kasar.

Shugabannin tsaron sun hada da: Mai bada shawara ga shugaban kasa a kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno, shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin.

Sauran sune sifeta janar din 'yan sanda, Mohammed Adamu da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, Yusuf Bichi.

Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa shugabannin tsaro kiran gaggawa
Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa shugabannin tsaro kiran gaggawa Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

An yi kiran gaggawar ne bayan bukatar da Sada Soli ya mika gaban majalisar na yin hakan sakamakon hauhawar al'amuran 'yan bindiga a yankin arewa ta tsakiya da arewa maso gabas.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga hukumomin rundunar sojin kasar nan da su dauka karin dakaru 100,000 na soji don maye gurbin rashin sojin da kasar nan don kawo karshen kalubalen tsaro.

Sun kara kira ga rundunar sojin kasar nan da ta kira jami'anta da suka yi murabus matukar suna da lafiya kuma basu wuce shekaru 50 ba kamar yadda bangare na VII, sashi na 25 ya amince.

Wannan na daga cikin kira da kwamitin majalisar mai bincikar kisan Auno da ta faru a watan Fabrairu suka yi.

Shugaban kwamitin kula da rundunar soji, Abdulrazak Namdaz, wanda ya mika rahoton gaban majalisar, ya ce ba a ba matafiya wani tsaro ta hanyar saka sojin a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

A yayin mika rahoto, Namdaz ya ce bincikensu ya bankado cewa matafiya ne aka tare da kauyen Auno bayan sun ki bin dokar hana walwala da aka saka a kauyen.

Wannan lamarin ne yasa mayakan Boko Haram suka samu damar halaka mutane birjik.

"A dayan bangaren kuma, da sojojin sun bai wa matafiyan kariya, da ba a rasa rayuka masu yawan hakan ba.

"Da kuma an yi nasarar kama wa ko kashe wasu daga cikin 'yan ta'addan ba tare da an samu yawan mamata a cikin matafiyan ba.

"Hakan ya faru ne saboda rundunar sojin bata da jami'ai masu yawa da za su iya kai mayakan ta'addancin kasa a wasu kauyukan, shiyasa dakarun marasa yawa ake cin galabarsu.

"Ta hanyar diban sojoji, za a maye wannan gurbin na rashin ma'aikata."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel