COVID-19: Gwamnan Kogi ya yi watsi da rahoton NCDC

COVID-19: Gwamnan Kogi ya yi watsi da rahoton NCDC

Gwamnatin jihar Kogi ta musanta karuwar mai cutar korona da hukumar yaki da hana cututtuka masu yaduwa ta bayyana a jihar na ranar 3 ga watan Yuni.

Alkalumman hukumar NCDC ta sanar da samun karuwar masu cutar korona 348 a fadin Najeriya a ranar 3 ga watan Yuni.

Kamar yadda hukumar ta fitar, jihar Legas ta samu karin mutane 163, babban birnin tarayya na da karin mutum 76 sai jihar Ribas da ta samu karin mutum 21.

Ta kara da cewa, jihohin Delta, Nasarawa da Neja sun samu karin mutane takwas-takwas yayin da Enugu ke da karin mutum shida.

COVID-19: Gwamnan Kogi ya yi watsi da rahoton NCDC
COVID-19: Gwamnan Kogi ya yi watsi da rahoton NCDC Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Jihar Binuwai na da karin mutum hudu, Ogun na da karin biyu. Jihohin Osun, Filato, Kogi da Anambra na da karin mutum daddaya.

Amma kuma, a wallafar da kwamishinan lafiya na jihar Kogi, Dr Saka Haruna yayi, ya ce ma'aikatar da gwamnatin jihar basu san wani wanda ya sake kamuwa da cutar korona ba.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Gwamna Masari ya dakatar da daukar aiki, gudanar da manyan ayyuka da karin girma a Katsina

Ya bayyana karin mutum daya da NCDC ta bayyana daga jihar a matsayin bogi.

"Mutum daya da aka ce ya kara kamuwa da cutar a jihar gaskiya bamu sani ba. Bamu san inda aka yi gwajin ba," ya rubuta.

Akwai wata artabu da ake yi tsakanin gwamnatin jihar Kogi da NCDC a kan rashin yarda.

Gwamnatin jihar Kogi ta zargi NCDC ta mayar da annobar korona kasuwanci, lamarin da Yahaya Bello ya ce ba zai shiga ba.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan jihar Yahaya Bello na jihar Kogi, ya shimfida dokar kulle a wani bangare na jihar biyo bayan samun bullar cutar korona.

Gwamnan ya yi riko da gargadin da Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa a kasar NCDC ta yi, inda cikin gaggawa ya shimfida dokar kulle a gaba daya karamar hukumar Kabba-Bunu.

Gwamna Bello ya yanke hukuncin da ya zartar a kan karamar hukumar Kabba-Bunu cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin 1 ga watan Yuni.

Sanarwar da babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin Kogi, Onugwo Muhammed ya gabatar wa da jaridar Legit.ng, ya bayyana cewa ko shige-da-fice a tsakanin gida-zuwa-gida ya haramta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel