Covid-19: NNPC ta kaddamar da manhajar gano wadanda sukayi mu'amala da masu cutar

Covid-19: NNPC ta kaddamar da manhajar gano wadanda sukayi mu'amala da masu cutar

Kamfanin man fetur ta kasa (NNPC) ta ce ta samar da manhajar zakulo wadanda suka yi ma'amala da masu cutar korona wacce za a iya amfani da ita a sassa daban-daban a fadin kasar nan.

Kamfanin ta bayyana hakan a wata takarda da ta fitar ta hannun kakakinta, Dr Kennie Obateru, a Abuja a ranar Laraba.

Kamar yadda yace, wannan yana daga cikin kokarin kamfanin na amfanin da kimiyyar yada labarai da sadarwa.

Manajan daraktan kamfanin a bangaren yada labarai, Danladi Inuwa, ya ce manhajar na daga cikin kokarin kamfanin na dakile yaduwar annobar a cikin ma'aikatu, sassa da cibiyoyin gwamnati.

Covid-19: NNPC ta kaddamar da manhajar zakulo masu cutar
Covid-19: NNPC ta kaddamar da manhajar zakulo masu cutar Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

"Manhajar a halin yanzu an kammala ta kuma an saka ta a sassa daban-daban na kamfanin wanda zai bayyana dukkan bayanai a kan bako ko jami'i.

"Idan akwai wani kalubale na lafiya, masana kiwon lafiyar kamfanin za su iya gano mara lafiyar ta bayanai da aka samu ta hanyar amfani da manhajar," Inuwa yace.

KU KARANTA KUMA: An sanar da rasuwar tsohon Gwamnan Jihar Ondo Bamidele Olumilua

Ya kara da cewa, ma'aikatan matatar za su iya amfani da manhajar a gidajensu wajen adana bayanan baki, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Inuwa ya ce, kamfanin za ta yi amfani da manhajar wurin siyarwa tare da rarrabe man fetur da kayayyakinsu.

Da wannan manhajar, za a iya duba dukkan kayayyakin man fetur da aka shigo da su, ko aka siyar a kowanne lokaci.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labarin na daban, hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce za ta ci gaba da gwaji a kan hydrochloroquine (maganin zazzabin cizon sauro), domin maganin cutar korona.

A ranar 22 ga watan Mayu, mujallar kiwon lafiya ta The Lancet, ta wallafa cewa maganin zazzabin cizon sauro (chloroquine) ba ya da tasiri wajen magance cutar korona.

The Lancet ta yi ikirarin cewa, chloroquine bai yi ingantaccen tasiri ba a kan mutane 96,032 masu cutar korona da aka yi gwajin maganin a kansu.

Kwanaki uku bayan wannan wallafa, Tedros Ghebreyesus, shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya, ya bada sanarwar a dakatar da gwaji a kan maganin na chloroquine.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel