A lokacina ne NPA ta zubawa asusun tarayya kudin da ba a taba ji ba – Usman

A lokacina ne NPA ta zubawa asusun tarayya kudin da ba a taba ji ba – Usman

Hadiza Bala Usman, wanda ita ce shugabar hukumar NPA ta kasa, ta ce a karkashin shugabancin ta ne gwamnatin tarayya ta samu makudan kudin da ba ta taba samun irinsu a tarihi ba.

Hajiya Hadiza Bala Usman ta bayyana cewa a jagorancinta ne hukumar NPA ta zubawa asusun gwamnatin tarayya kudin shigan da ya fi na kowane gwamnati da aka yi a baya yawa.

Bala Usman ta yi wannan bayani ne lokacin da aka yi hira da ita a gidan jaridar TVC ranar Talatar nan.

A bayaninta, shugabar ta NPA ta bayyana ayyukan da ta yi a cikin shekara hudu.

Da ta ke magana game da wa’adinta, ta ce: “Kudin da mu ke tatsowa gwamnati ya karu. Abin da mu ka zuba a asusun gwamnatin tarayya shi ne mafi yawa da aka taba samu daga NPA."

“Don haka tashoshin ruwa da ma Najeriya ta samu shekaru hudu masu amfani.” Usman ta kara da cewa: “Hukumar ta tashi tsaye, ta kara kokari wajen gudumuwar da ta ke badawa”

KU KARANTA: Hukumar NAHCON ta na sauraron Saudi game da aikin hajjin bana

A lokaci na ne NPA ta zubawa asusun tarayya kudin da ba a taba ji ba – Usman
Hadiza Bala Usman Hoto: Twitter
Asali: Instagram

A cewar Hadiza Bala Usman, NPA ta kara kaimi a shekaru hudu da ta yi ta na jan ragamar hukumar. Duk da haka ta ce hukumar kasar ta na fama da kalubalen da ba za a rasa ba.

Daya daga cikin abubuwan da su ke jawowa Najeriya cikas shi ne rashin tasoshin ruwa masu zurfi da za su iya cin manyan jirage. Yanzu ana kokarin ganin an samu wannan a kasar.

Shugabar da aka karawa wa’adi ta ce za ta dage wajen ganin Najeriya ta samu tashoshi masu zurfi nan ba da dadewa ba. Idan ba za ku manta ba, ana gina irin wannan tasha a garin Lekki.

“Tafiyar ta kasance mai ban sha’awa da kuma kalubale a ‘yan wasu wurare, amma dai an yi nasara a hanya. Mun ga yadda tashoshin ruwan kasar su ka cigaba.” Inji Bala Usman.

Ta ce: “Zan so in yi magana game da gudumuwar da mu ke ba CRF, lokacin da mu ka zo an ba gwamnatin tarayya kusan N18b ne, amma mun ba (gwamnati) N30b a 2017 da 2018."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel