Cutar COVID-19 ce ta kashe Darektanmu a makon jiya – Inji Hukumar NDDC

Cutar COVID-19 ce ta kashe Darektanmu a makon jiya – Inji Hukumar NDDC

- Cutar Coronavirus ta kashe wani Daretan kudi a NDDC a makon da ya gabata

- Hukumar ta ce ta rufe ofis bayan rasuwar Ibanga Bassey Etang a Jihar Ribas

A yayin da wadanda cutar COVID-19 ta kama a Najeriya su ka haura mutane 11, 000, mun samu labarin cutar ta kashe wani babban jami’i da ke aiki da hukumar NDDC ta kasa.

Hukumar NDDC da aka kafa domin kawo cigaba a yankin Neja-Delta ta bada sanarwar cewa wannan muguwar cuta ta Coronavirus ta kashe mata mista Ibanga Bassey Etang.

Kafin mutuwar Ibanga Bassey Etang, ya kasance darektan kudi da shugabanci a hukumar NDDC. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a jiya ranar Laraba, 3 ga watan Yuni.

NDDC ta fitar da jawabi na musamman a farkon makon nan, inda ta tabbatar da cewa COVID-19 ce ta yi sanadiyyar mutuwar jami’in na ta kwastsam ranar Alhamis din da ta gabata.

KU KARANTA: Masu cutar Coronavirus sun karu da mutum 340 a Najeriya

Cutar COVID-19 ce ta kashe Darektanmu a makon jiya – Inji Hukumar NDDC
Hukumar NDDC
Asali: Facebook

Mista Charles Odili ne ya yi jawabi a madadin hukumar NDDC. A dalilin haka yanzu an rufe hedikwatar hukumar, an kuma bukaci ma’aikata su killace kansu daga jama’a.

Charles Odili ya shaidawa jaridar cewa an kai Ibanga Bassey Etang asibiti ne a ranar Alhamis bayan ya fara rashin lafiya, amma jim kadan da kwantar da shi kenan ya cika.

A cewar Odili, marigayin ya rasu ne asibitin koyar da aikin likita na jami’ar jihar Ribas sa’o’i uku bayan an kwantar da shi. Likitoci sun tabbatar da cewa COVID-19 ce ta kama shi.

Majiyar ta jaridar Daily Trust ta bayyana mana cewa an garzaya da wannan jami’in gwamnati asibitin da kimanin karfe 2:00 na tsakar dare, zuwa asuba ya ce ga garinku nan.

Rahotanni sun ce a halin yanzu babu mai zuwa aiki a babban ofishin hukumar. Ana sa ran cewa za ayi wa ma’aikatan na NDDC gwajin kwayar COVID-19 domin tabbatar da lafiyarsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel