Yanzu-yanzu: An samu karin mutum 348 masu dauke da korona

Yanzu-yanzu: An samu karin mutum 348 masu dauke da korona

Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa suka bayyana na ranar 3 ga watan Yunin 2020, an samu karin mutum 348 da ke dauke da cutar korona a Najeriya.

Kamar yadda ta bayyana, a jihar Legas an samu karin mutum 163, babban birnin tarayya an zakulo karin mutum 76 yayin da jihar Ebonyi ke da karin mutum 23.

Jihar Ribas na da karin mutum 21 sai jihohin Delta, Nasarawa da Niger ke da karin mutum takwas-takwas.

Jihar Enugu da ke kudancin Najeriya na da karin mutum 6 sai jihohin Bauchi, Edo, Ekiti, Ondo da Gombe sun samu karin mutum biyar-biyar.

Jihar Benue na da karin mutum 4, jihar Ogun na da karin mutum 2 sai jihohin Osun, Filato, Kogi da Anambra da ke da karin mutum daddaya.

A halin yanzu, jimillar masu cutar korona a fadin Najeriya ta kai 11166. An sallama mutum 3329 daga asibiti bayan warkewarsu yayin da 315 suka mutu sakamakon annobar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel