Mu na fuskantar karancin kudi da kayan aiki - Ministan tsaro
Bashir Salihi Magashi, ministan tsaro, ya ce rashin karfin runduna da karancin kudi na daga cikin manyan kalubale da su ka hana rundunonin tsaro katabus.
Da ya ke magana da manema labarai, Magashi ya ce wannan matsala na daga cikin abubuwan da ya gabatar yayin taron majalisar zartarwa na mako - mako da aka gudanar yau, Laraba.
Shugaban kasa, Muammadu Buhari, ne ya jagoranci taron da aka yi ta hanyar amfani da fasahar kiran waya mai nuna bidiyo.
"Mun yi magana a kan matsalolinmu. Mun yi magana a kan karancin ma'aikata, karancin kudin da ake warewa ma'aikatar tsaro.
"Mun yi magana a kan atisaye daban - daban da mu ka kaddamar, nasarorin da aka samu da akasin haka a karkashin kowanne atisaye daga Ofireshon Lafiya Dole zuwa Ofireshon Tawase.
"Mun yi magana a kan nakasun da kowanne atisaye ya samu, hatta mambobi sun tofa albarkacin bakinsu, kuma ina ganin nan bada dadewa ba za a ga sauyi a yanayin yadda mu ke gudanar da harkokinmu a ma'aikatar tsaro," a cewarsa.
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa kungiyar Boko Haram ta yi rashin wasu manyan kwamandoji, makusanta ga shugaban kungiyar, Abubakar Shekau.
A cewar rundunar soji, an kashe manyan kwamandojin tare da sauran dumbin mayakan kungiyar Boko Haram yayin wata musayar wuta mai zafi da aka yi tsakaninsu a ranar 26 ga watan Mayu.
DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan PDP ya koma jam'iyyarsa bayan ya shafe shekaru 6 a APC
An yi musayar wutar ne bayan reshe ya juye da mujiya a harin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kai a kan rundunar soji a kwanar Banki.
Daga cikin gagararrun kwamandojin kungiyar Boko Haram da dakarun soji su ka kashe akwai; Manzar Halid, Abu Fatima.
Wata majiyar rundunar soji mai tushe ta tabbatar da cewa an kashe mambobin kungiyar Boko Haram 70 tare da wasu manyan kwamandojin kungiyar irinsu ABu Jamratul Al-Naweer, Kaka Bana da Tareta Babakari.
Kazalika, sojoji sun kwace kayayyaki da makaman mayakan kungiyar da su ka hada da motocin yaki, babura da Kekuna.
Sojoji sun lalata kayayyakin da makaman a yayin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka janye jiki tare da tarwatsewa zuwa cikin jeji.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng