COVID-19 ta kashe hadimi a fadar gwamnan Gombe, an rufeta ana shirin feshi

COVID-19 ta kashe hadimi a fadar gwamnan Gombe, an rufeta ana shirin feshi

Wani ma'aikacin gidan gwamnatin jihar Gombe ya rasu sakamakon annobar korona, lamarin da yasa aka rufe ofishin sakataren gwamnatin jihar tare da bada umarnin yin feshi a asibitin gidan.

Shuaibu Danlami darakta ne na ayyuka na musamman da siyasa a ofishin sakataren gwamnatin jihar kuma ya rasu a ranar Lahadi bayan gajeriyar rashin lafiya, kwamitin yaki da annobar korona ta jihar ta sanar.

An diba samfur dinsa wanda sakamakon ya bayyana cewa yana dauke da cutar korona a ranar Talata, shugaban kwamitin, Idris Mohammed ya sanar a ranar Laraba.

COVID-19 ta kashe hadimi a fadar gwamnan Gombe, an rufeta ana shirin feshi
COVID-19 ta kashe hadimi a fadar gwamnan Gombe, an rufeta ana shirin feshi Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya ce ofishin sakataren gwamnatin da gidan gwamnatin duk za a kulle su don yin feshi tare da daukar samfur din dukkan ma'aikatan don gwaji.

KU KARANTA KUMA: Duk mamban da ya karba mukami daga PDP, ya bar jam'iyya - APC ta ja kunnen mambobinta

Danlami mamba ne kuma mataimakin sakataren kwamitin yaki da cutar na jihar kuma an dauka samfur din dukkan 'yan kwamitin.

A halin yanzu, jami'ai na kokarin zakulo wadanda suka yi mu'amala da mamacin. Ana shirin zakulo su, yi musu gwaji da kuma killace duk wanda ya halarci jana'iza ko makokin Danlami.

Danlami ne mutum na bakwai da ya rasu sakamakon annobar korona a jihar Gombe.

An sallami wasu mutum 125 daga cibiyar killacewa bayan warkewa da suka yi amma mutum 23 na cibiyar.

Ya ce tunda mamacin mamba ne kwamitin yaki da cutar korona na jihar, za a tantance tare da yi wa 'yan kwamitin gwajin cutar.

A gefe guda, mun ji cewa kwamitin kar ta kwana da gwamnatin jihar Gombe ta kafa domin lura da annobar cutar korona, ta ce a halin yanzu an samu mutum 7 da cutar ta hallaka a fadin jihar.

Farfesa Idris Muhammad, shugaban kwamitin, shi ne ya sanar da hakan cikin birnin Gombe yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba, 3 ga watan Yuni.

Farfesa Muhammad ya ce mutum uku cikin bakwai din da suka riga mu gidan gaskiya, sun kamu da cutar ne ba tare da sun fita daga cikin jihar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel