An kai hari sansanin soji a cikin Amurka, an kashe biyu

An kai hari sansanin soji a cikin Amurka, an kashe biyu

- An kai hari sansanin sojojin sama na kasar Amurka da ke jihar North Dakota da safiyar ranar Laraba

- An kashe biyu saga cikin sojojin yayin harin da aka kai ta hanyar bude wuta a sansanin sojojin

- Sansanin sojojin sama na Grand Forks da ke jihar North Dakota ne ya fara fitar da sanarwar kai harin

Jaridar Trt da ke yanar gizo ta rawaito cewa an kashe sojojin kasar Amurka guda biyu yayin wani hari da aka kai sansanin sojojin sama da ke jihar Dakota ta arewa.

Trt ta ce ta samu labarin kai harin ne daga wata sanarwa da sansanin sojojin sama na Grand Forks da ke jihar Dakota ya fitar.

"Da safiyar yau (Laraba) ne aka kai hari a sansanin sojojin sama da ke jihar North Dakota. An bude wuta a sansanin sojojin, lamarin da ya yi sanadiyar dakarun soji biyu," a cewar sanarwar.

Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara bincike a kan kai harin tare da sanar da cewa za a bayyana sunayen sojojin da aka kashe a cikin sa'o'i 24.

Sai dai, sanarwar ba ta bayyana wadanda ake zargi da kai harin ba. Kazalika, sanarwar ba ta nuna cewa an kama wani ko zargin wata kungiya da ke da hannu wajen kai harin ba.

Kasar Amurka ta yamutse da zanga - zanga sakamakon kisan wani bakar fata, George Floyd, da jami'an 'yan sanda su ka yi.

An kai hari sansanin soji a cikin Amurka, an kashe biyu
Sojojin kasar Amurka
Source: UGC

Ma su zanga - zanga sun mamaye kusan manyan biranen kasar Amurka domin neman a hukunta 'yan sanda da su ka yi wa Floyd kisan gilla a bainar jama'a.

DUBA WANNAN: Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe mutane 9, sun raunata wasu da dama a sabon harin da su ka kai

Duk da kasar Amurka ta saka dokar hana zirga - zirga domin shawo kan zanga - zangar da ta barke a kasar, hakan bai sa ma su zanga - zangar sun bar kan tituna da wuraren da su ka mamaye ba.

A ranar Talata ne shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar cewa zai yi amfani da sojoji domin tarwatsa ma su zanga - zangar da ke barazanar shiga fadar gwamnati ta karfi.

Zanga - zangar neman a yi wa Floyd adalci ta hanyar hukunta 'yan sanda da su ka kashe shi, ta yadu zuwa kasashen duniya da dama, musamman a yankin nahiyar Turai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel