Gobara: Jami’an Hukumar kwana-kwana sun yi wa mutane 73 rai a Kano

Gobara: Jami’an Hukumar kwana-kwana sun yi wa mutane 73 rai a Kano

Jaridar Daily Trust ta rahoto hukumar kwana-kwana ta jihar Kano ta bayyana adadin mutane da kuma irin dukiyar da ta ceta daga gobara a cikin wata guda.

Mai magana da yawun bakin hukumar kashe gobara, ya ce akalla mutane 73 hukumar ta kawowa agaji a gobara 56 da aka yi a jihar Kano a cikin wata guda.

Alhaji Saidu Muhammed ya kuma bayyana cewa hukumar ta Kano ta yi kokarin hana asarar kaya na Naira miliyan 704 a cikin wannan lokaci da aka ambata.

Saidu Muhammed ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya fitar a Kano kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Vanguard a yau Larabar da rana.

“A watan Mayun 2020, mun samu gobara 56, daga cikinsu an samu rahotannin bogi 17. Mun rasa mutane 17 a haduran, yayin da mu ka ceci mutane 73.” Inji sa.

“Mun yi asarar dukiya ta N85, 575, 000, sannan kuma mun ceto kaya wanda darajar su ya kai N704, 100, 000.” Jaridar ce ta fitar da wannan rahoto dazu nan.

KU KARANTA: An kai wani hari a Kaduna, an bindige mutane 9, an yi wa wasu rauni

A cewar Alhaji Saidu Muhammed, ana yawan samun gobara ne daga hadarin motoci a titi, da amfani da na’urorin wuta, da kuma rijiyoyi da ake bari a bude.

Kakakin hukumar kwana-kwanan ta gargadi iyaye su rika kula da ‘ya ‘yansu. Muhammed ya ja-kunnen iyayen da su ke barin yaransu su na zuwa iwo a ruwa.

Bayan haka, jami’in hukumar ya yi kira na musamman ga mutanen jihar Kano su yi hankali da wasa da wuta, wanda hakan ya na iya jawo mummunan gobara.

"A cikin watan Mayun da ya gabata, an rasa dukiyar Naira miliyan 85.5 a jihar Kano. Bayan asarar makudan kudi, mutane 17 su ka mutu a dalilin gobarar da aka yi."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel