Zaben fidda dan takara: Gwamna Obaseki ya gargadi Oshimhole

Zaben fidda dan takara: Gwamna Obaseki ya gargadi Oshimhole

Gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki, ya gargadi shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshimhole, a kan kokarin kawo katsa landan a zaben fidda dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Edo.

Jam'iyyar APC ta tsayar da ranar 22 ga watan Yuni a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben fidda dan takararta na gwamna a babban zaben gwamnan jihar Edo da za a yi a watan Oktoba.

Obaseki ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da ya mayar da fom dinsa na takarar gwamna a hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa da ke Abuja.

"Ina kira ga Oshiomhole da ya nesanta kansa daga kawo katsa landan a harkar zaben dan takarar gwamnan jihar Edo saboda ya na da dan takara," a cewarsa.

Kazalika, gwamna Obaseki ya bayyana shirinsa na shiga kowanne irin zaben fidda dan takara da uwar jam'iyyar APC ta shirya matukar za a bi tsarin kundin mulkin jam'iyya ba tare da wata rufa - rufa ba.

A ranar Litinin Obaseki, mai fama da rikicin cikin gida a jam'iyyar APC, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, domin gabatar ma sa da fom dinsa na sake neman takarar gwamna a karo na biyu.

Jim kadan bayan kammala ganwarsa da shugaba Buhari, Obaseki ya shaidawa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa, "shugaba Buhari ya ba ni tabbacin samun goyon bayansa."

An dade ana nuna yatsa tare da musayar maganganu marasa dadi a tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

Zaben fidda dan takara: Gwamna Obaseki ya gargadi Oshimhole
Obaseki da Oshimhole
Asali: UGC

A yayin ziyarar, Obaseki ya shaidawa Buhari cewa mutanen jihar Edo su na goyon bayansa kuma a shirye su ke su sake zabensa.

Ziyarar da Obaseki ya kaiwa Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage saura sati uku a gudanar da zaben fidda dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar da za a yi a cikin watan Oktoba na shekarar nan.

DUBA WANNAN: Sulhu da 'yan bindiga: Masari ya bayyana wadanda su ka ci amanar gwamnatinsa

Obaseki na fuskantar barazana daga Osagie Ize - Iyamu, tsohon dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP da ake tunanin ya na da goyon bayan Oshiomhole; tsohon gwamnan Edo kuma tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC).

Da ya ke magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, Obaseki ya ce ya kaiwa Buhari ziyara ne domin sanar da shi aniyarsa ta sake yin takarar kujerar gwamnan jihar Edo.

"Shugaban kasa ya karbeni hannu bibiyu, ya karramani sosai. Ya duba fom dina na takara da na nuna ma sa, ya yi min fatan alheri tare da bani tabbacin samun goyon bayansa," a cewar Obaseki.

Ziyarar ta Obaseki na zuwa ne kwana daya kacal bayan ganawarsa da Tinubu da wasu sauran gwamnonin jam'iyyar APC a jihar Legas.

Tinubu ya kasance makusanci ga Oshiomhole, hasali ma shine ya kawo shi takarar kujerar shugabancin jam'iyyar APC bayan karewar wa'adin tsohon jam'iyyar, John Oyegun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng