Tsohon gwamnan PDP ya koma jam'iyyarsa bayan ya shafe shekaru 6 a APC
Wani kwamitin sulhu da jam'iyyar PDP reshen jihar Ekiti ta kafa ya sanar da cewa tsohon gwamnan jihar, Segun Oni, ya koma tsohuwar jam'iyyarsa bayan ya shafe tsawon shekaru 6 a jam'iyyar APC.
Kwamitin ya bayyana cewa ya yi matukar farin cikin samun nasarar shawo kan Oni har ya amince ya dawo jam'iyyar PDP tare da 'yan gani kashenin magoya bayansa.
A cewar kwamitin, dawowar Oni ba kankanuwar nasara ba ce ga mambobin kwamitin da shugabanci jam'iyyar PDP na jihar Ekiti.
Kazalika, kwamitin ya yi kira ga tsohon ministan aiyuka, Sanata Adedayo Adeyeye, da sauran wadanda su ka bar PDP da su dawo jam'iyyar.
Adeyeye ya fice daga jam'iyyar PDP ana daf da gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti a shekarar 2018 bayan ya sha kasa a hannun Farfesa Kolapo Olusola a zaben fidda dan takarar jam'iyyar PDP.
Bayan fitarsa daga PDP, Adedeye ya koma jam'iyyar APC inda ya hada kai da dan takararsu, Dakta Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti mai ci.
Da su ke ganawa da manema labarai ranar Litinin a Ado-Ekiti, shugaban kwamitin, Sanata Hosea Agboola, da sakatarensa, Diran Odeyemi, sun gargadi sauran mambobin jam'iyyar PDP a kan nuna wata halayya da kan iya kawo nakasu a kokarin sulhun da ake yi.
Agboola, tsohon dan majalisar wakilai ta kasa, ya yi watsi da jita - jitar da ake yadawa a kan cewa kwamitinsu ya na aiki ne domin taimakon tsagin jam'iyyar PDP da ke hamayya da tsohon gwamnan jihar, Ayodele Fayose.
A kwanakin baya ne Fayose ya bayyana cewa jam'iyyar PDP a Ekiti ba ta maraba da Oni, saboda bashi da wani sauran tasiri a siyasa.
DUBA WANNAN: Kungiyar Boko Haram ta yi rashin manyan kwamandoji 5 na hannun daman Shekau
A shekarar 2014 ne tsohon gwamna Oni ya fita daga jam'iyyar PDP tare da sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Sai dai, APC ta dakatar da Oni daga mukaminsa na shugaban jam'iyyar na yankin kudu maso yamma bisa zarginsa da rashin mutunta tsarin jam'iyya.
APC ta nada shugaban rikon kwarya tare da yin burus da al'amuran Oni duk da korafin da ya ke yi a kan cewa ba a bashi girma da kimar da ya kamata ya samu a jam'iyyar.
Ko a 'yan watannin da su ka gabata, sai da Oni ya yi barazanar cewa zai fita daga jam'iyyar APC matukar aka cigaba da yi ma sa rikon wasarairai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng