Covid-19: Jihohi 4 da suka yi watsi da umarnin FG na bude wuraren bauta

Covid-19: Jihohi 4 da suka yi watsi da umarnin FG na bude wuraren bauta

Gwamnatin tarayya ta saka dokar hana taruwa a wuraren bauta a matsayin hanyar dakile yaduwar annobar coronavirus a Najeriya.

Amma kuma, bayan shawarar da kwamitin yaki da annobar korona ta kasa ta bayar, gwamnatin tarayya ta sanar da sassauta dokar daga ranar Litinin, 1 ga watan Yuni.

PTF ta bayyana cewa an yanke wannan hukuncin ne bayan jihohi sun aminta da tsare-tsaren da NCDC ta fitar.

A wani ci gaba, gwamnatocin wasu jihohi sun bayyana cewa ba su dage dokar hana tarukan addinai a fadin jihar sakamakon kalubalen da ake fuskanta a sakamakon annobar.

Covid-19: Jihohi 4 da suka yi watsi da umarnin FG na bude wuraren bauta
Covid-19: Jihohi 4 da suka yi watsi da umarnin FG na bude wuraren bauta Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: COVID:19: Ingila ta haramta jima'i da wanda ba dan gida ba a yayin kulle

Legit.ng ta tattara wasu jihohi da suka yi suka ga hukuncin gwamnatin tarayya na dage dokar hana tarukan addinai. Ga jihohin:

1. Legas: Babu shakka jihar Legas ce cibiyar korona ta Najeriya. Tana da mutum 5,277 da ke dauke da cutar inda mutum 67 suka mutu.

Wannan al'amarin ne yasa gwamnan jihar ya bayyana cewa babu batun bude masallatai da majami'u.

2. Kaduna: Jihar Kaduna na da mutum 297 da suka harbu da cutar kuma ita ce ta 7 a jerin jihohin da suka fi yawan masu cutar a Najeriya.

A martanin gwamnatin jihar, ta sanar da cewa lokacin bude kasuwanni da wuraren bauta bai yi ba a jihar.

3. Kwara: Jihar Kwara na daya daga cikin jihohin arewa ta tsakiya da cutar ta abkawa. Kwamishinan lafiya na jihar, Raji AbdulRazaq ya ce duk da gwamnatin tarayya ta bada umarnin bude wuraren bauta da kasuwanni, ya rage wa jihar ta aiwatar da abinda ya kamata.

4. Osun: Jihar Osun ta yi martani a kan umarnin da gwamnatin tarayya ta bada na bude kasuwanni da wuraren bauta. Jihar za ta samu tattaunawa da shugabannin addinai don samun kaiwa matsaya.

A gefe guda mun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta amince da bude filayen jiragen sama biyar don dawo da zirga-zirgar jirage a cikin kasar nan daga ranar 21 ga watan Yuni.

Kaftin Musa Nuhu, shugaban hukumar sufurin jiragen sama (NCAA) ya sanar da hakan a wata wasika mai kwanan watan 1 ga Yunin 2020, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta bayyana cewa, an rufe filayen jiragen saman ne don dakile yaduwar muguwar cutar coronavirus kuma za a ci gaba da hana tashi ko saukar jiragen ketare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel