Buhari ya nada sabon kwamishinan INEC a jihar Osun

Buhari ya nada sabon kwamishinan INEC a jihar Osun

A ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nemi majalisar dattijai ta tabbatar da nadin Dakta Tella Adeniran Rahamon a matsayin sabon REC, wato kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), a jihar Osun.

Kazalika, shugaba Buhari ya aika sunan James Jiya Kolo a matsayin wanda zai maye gurbin marigayi Daniel James Kolo, wanda aka aika sunansa a matsayin mamba a FCC daga jihar Kwara amma ya mutu kafin a tabbatar da su.

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ne ya karanta wasikun da shugaba Buhari ya aika yayin zaman majalisar na yau, Talata, 2 ga watan Yuni.

Lawan ya mika bukatun shugaba Buhari zuwa kwamitocin da ke da alhakin dubasu domin daukan matakin majalisa na gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel