Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin hauhawar adadin ma su kamuwa da korona

Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin hauhawar adadin ma su kamuwa da korona

- Ana samun hauhawar alkaluman ma su kamuwa da cutar korona a jihar Kaduna a 'yan kwanakin baya bayan nan

- Gwamnatin jihar ta ce jami'anta na bi gida - gida domin neman wadanda su ka kamu da kwayar cutar korona

- An tabbatar da bullar annobar korona a kananan hukumomin jihar Kaduna guda tara

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce jami'anta sun ziyarci gidaje 29,771 a kananan hukumomi tara da aka tabbatar da bullar annobar cutar korona.

Yin hakan na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na kara matsin lamba wajen neman wadanda su ka kamu da cutar korona, a cewar kwamishinar lafiya, Dakta Amina Mohammed Baloni.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa kananan hukumomin da aka tabbatar da bullar annobar cutar korana a jihar Kaduna sune kamar haka; Chikun, Igabi, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, Makarfi, Giwa, Sabon Gari, da Zaria.

A sanarwar da jihar ta fitar ta hannun ma'aikatar lafiya, ta bayyana cewa jami'anta na shiga lunguna suna neman mutanen da rashin lafiyarsu ke kama da na ciwon cutar korona domin a yi mu su gwaji.

Ma'aikatar ta bayyana cewa ma'aikatan lafiya sun gwada mutane 297 bayan sun nuna alamun kamuwa da cuta mai saka zazzabi da mura.

Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin hauhawar adadin ma su kamuwa da korona
Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin hauhawar adadin ma su kamuwa da korona
Asali: Twitter

"Mu na yin wannan gwaji ne a kan wadanda ake zargin sun yi mu'amala da mai dauke da cutar korona da kuma kara neman sabbin wadanda su ka kamu da cutar ta wata hanyar daban ko kuma wadanda alamomin rashin lafiyarsu su ka yi kama da na mai cutar korona," a cewar Dakta Amina.

DUBA WANNAN: Buhari ya gana da kwamitin yaki da annobar korona a kasa (Hotuna)

Dakta Amina ta yi gargadin cewa adadin ma su dauke da cutar korona a Kaduna zai cigaba da hauhawa saboda karuwar yawan gwajin da ake yi wa jama'a a jihar.

"Yin irin wannan gwaji zai bayar da damar gano ma su dauke da kwayar cutar tun kafin ta girmama, hakan zai bada damar killace wadanda su ka kamu tare da duba lafiyarsu cikin sauki," a cewarta.

A cewar Dakta Amina, ya zuwa ranar 31 ga watan Mayu, jihar Kaduna ta samu adadin mutane 258 da aka tabbatar sun kamu da cutar korona, an sallami mutane 157 bayan sun warke sarai, akwai mutane 93 a cibiyar killacewa, mutane 8 kuma sun mutu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel