Kano: Har yanzu babu fita ranakun Litinin, Talata, Alhamis da Asabar — Ganduje

Kano: Har yanzu babu fita ranakun Litinin, Talata, Alhamis da Asabar — Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano ta ce har yanzu dokar kulle tana aiki a jihar a ranakun Litinin, Talata, Alhamis da Asabar.

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan matakin domin biyaya ga umurnin gwamnatin tarayya na sassauta dokar kullen da aka saka domin dakile yaduwar COVID-19 a kasar nan.

Ta kuma fitar da sabbin kaidoji da dokoki kan yadda za a rika zuwa kasuwanni da wasu wuraren hada-hadan mutane a jihar don rage yiwuwar yada cutar korona.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Kano: Har yanzu babu fita ranakun Litinin, Talata, Alhamis da Asabar — Ganduje
Kano: Har yanzu babu fita ranakun Litinin, Talata, Alhamis da Asabar — Ganduje. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

Sanarwar ta ce bayan tuntubar kwararru a bangaren lafiya da bita kan halin da ake ciki a Kano, an bayar da izinin zirga-zirga da bude wuraren bauta a ranakun Lahadi, Laraba da Juma'a daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sabbin direktoci 6 da Buhari ya nada a NNPC

Ya ce gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya kira taron gaggawa tare da shugabanin kasuwanni don tattauna hanyoyin da za a tabbatar da bin dokokin kiyaye lafiya a kasuwannin.

Sanarwar ta cigaba da cewa akwai bukatar a tabbatar da bin dokoki a wuraren don kiyaye lafiyar mutane kamar saka takunkumi, samar da wuraren wanke hannu da sanitizers da duba zafin jikin mutane don gano masu alamun korona.

Kwamishinan ya ce duk da sassaucin da aka yi, har yanzu an hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi sai dai masu jigilar kayan abinci da wasu kayan amfanin yau da kullum.

Ya shawarci dalibai a jihar suyi amfani da damar da gwamnatin jihar ta bayar na daukan nauyin shirin koyar da su ta kafafen rediyo da talabijin.

Har wa yau, kwamishinan ya cigaba da cewa Ganduje ya danganta nasororin da aka samu ta bangaren raguwar yaduwar cutar a jihar ga matakan da gwamnati da hukumomin lafiya suka dauka tare da adduoi da malamai da mutanen jihar ke yi.

Ya kuma yi kira da a cigaba da adduo'i domin Allah ya kawar da cutar gaba daya daga jihar da duniya baki daya.

Mr Garba ya kuma yaba wa mutanen jihar bisa hakuri da juriya da suke yi duk da dokar takaita zirga-zirgan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel