Taron Tinubu da gwamnonin APC a Legas ya haifar da cacar baki
Batun ganawar sirri tsakanin jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, da gwamnonin jam'iyyar APC ya haifar da cacar baki mai zafi a dandalin sada zumunta.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa Tinubu ya kira taron ne domin sulhunta rigingimun cikin jam'iyyar APC da ke kara zurfi, musamman a jihar Edo.
An dade ana nuna yatsa tare da musayar maganganu marasa dadi a tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.
Taron na sirri, wanda aka yi ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, ya samu halartar shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, gwaman jihar Ondo; Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Legas; Babajide Sanwo-Olu.
Ragowar sun hada da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar GAnduje, Godwin Obaseki na jihar Edo, Simon Lalong na jihar Filato, Mai Mala Buni na jihar Yobe, Adeboyega Oyetola na jihar Osun, Badaru Abubakar na jihar Jigawa, da Abubakar Bello na jihar Neja.
Duk da ba a fitar da wani bayani a kan dalilin kiran taron da aka yi a gidan gwamnatin jihar Legas da ke Marina ba, wasu rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ne ya tunkari Tinubu tare da rokon ya shiga batun rikicinsa da tsohon maigidansa, Oshiomhole.
Rahotanni sun bayyana cewa Obaseki ya shiga damuwa bayan ya fahimci cewar Oshiomhole na shirya ma sa tuggun da zai iya jawo ma sa rasa kujerarsa a zaben fidda dan takarar gwamna na jihar Edo wanda za a yi a cikin watan Yuni.
DUBA WANNAN: Yadda tsohon gwamnan APC ya dinga biyan kansa alawus din N50m duk bulaguro zuwa Abuja
An samu sabanin ra'ayi a kan hanyar da za a gudanar da zaben fidda dan takara a tsakanin bangaren gwamna Obaseki da bangaren uwar jam'iyyar APC a karkashin jagorancin Oshiomhole.
A yayin da gwamna Obaseki ke son a yi amfani da wakilan jam'iyya domin gudanar da zaben, bangaren Oshiomhole sun kafe a kan a yi kato bayan kato.
Tinubu ya ce ya goyi bayan a gudanar da zaben fidda 'yan takara a cikin jam'iyya domin yin hakan shine tsarin dimokradiyya ta gaskiya da adalci, kuma ta hakan ne kawai dan takara zai gwada karbuwa da farin jininsa a wurin jama'a, wanda hakan shine al'adar siyasa.
Rahotannin sun bayyana cewa Tinubu ya nemi a yi wa gwamnonin da ke kan mulki da sauran ma su sha'awar takara adalci a yayin da ya ke jaddada cewa gudanar da zaben cikin gida zai kara karfafa dimokradiyya da bawa dan takara karfin gwuiwa.
Tuni mahawara da cacar baki mai zafi ta barke a dandalin sada zumunta a tsakanin 'yan Najeriya a kan ma'ana da nufin ganawar Tinubu da gwamnoni a Legas.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng