Sabon kasafin kudi: Tashin hankali da tarzoma ta barke a majalisar tarayya

Sabon kasafin kudi: Tashin hankali da tarzoma ta barke a majalisar tarayya

Zaman lafiya ya kaurace wa majalisar dattawan kasar nan tun bayan rashin jituwar da aka samu a makon da ya gabata wajen amince wa da kasafin kudin 2020 da ake gyara wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika gaban majalisa.

Majiyoyi daban-daban daga majalisar dattawan ta sanar da jaridar The Nation cewa kura ta tashi bayan shugaban majalisar, Ahmed Lawan ya mika bukatar aminta da takardun.

Sanatocin sun yi watsi da shawarar Lawan bayan sun bayyana dalilai kamar haka:

1. Bai wa sanatocin wa'adin mako daya ba dubawa tare da aminta da kasafin bayan an dauki watanni biyu ana gyara shi.

2. Ba wa kwamitin majalisar damar duba kasafin tare da bada shawara inda ya dace.

3. Boye kura-kurai wadanda kwamitocin da suka kamata ne kadai za su iya ganowa.

4. Duba wasu sashi tare da mantawa da wasu a cikin manyan ayyukan mazabu.

Sabon kasafin kudi: Tashin hankali da tarzoma ta barke a majalisar tarayya
Sabon kasafin kudi: Tashin hankali da tarzoma ta barke a majalisar tarayya Hoto: The Nation
Asali: UGC

An gano cewa wani daga cikin 'yan kwamitin kasafin kudin ya zabga wa mazabarsa har biliyan 12 na manyan ayyuka yayin da sauran suka samu tsakanin miliyan 300 zuwa 500.

Wannan ci gaba kuwa ya kawo tashin hankali inda da yawa daga cikin sanatocin suka bukaci adalci a al'amuran.

KU KARANTA KUMA: Satar kaji: Kotu ta daure saurayi da budurwarsa

Kamar yadda wata majiya ta bayyana, Lawan ya bukaci 'yan majalisar da su bada hadin kai wajen gaggauta aminta da sabon kasafin kudin don kuwa kasar nan na fuskantar kalubalen tattalin arziki. Taimakon 'yan majalisar ne kadai ake bukata a halin yanzu.

Ya bukaci sanatocin sa su amince da sabon kasafin a gobe Talata.

A wani labari na daban, hukumar NCAA mai kula da tashi da saukar jiragen sama a Najeriya ta na sa ran a dawo jigilar mutane a wasu daga cikin manyan tashoshin jirgin kasar nan da ‘yan kwanaki kadan.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto NCAA ta na cewa akwai yiwuwar a bude filin Murtala Mohammed da ke Legas, da filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya.

Bayan wani zama da hukumar NCAA ta yi a ranar Asabar da ta gabata, gwamnatin tarayya ta fara tunanin dawowa aiki a kasar. Za a fara ne da bude wasu manyan filayen jirgin sama tukun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel