NCAA: Tashoshin jirgin Legas, Abuja, Kano da Fatakwal za su dawo aiki

NCAA: Tashoshin jirgin Legas, Abuja, Kano da Fatakwal za su dawo aiki

Hukumar NCAA mai kula da tashi da saukar jiragen sama a Najeriya ta na sa ran a dawo jigilar mutane a wasu daga cikin manyan tashoshin jirgin kasar nan da ‘yan kwanaki kadan.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto NCAA ta na cewa akwai yiwuwar a bude filin Murtala Mohammed da ke Legas, da filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya.

Haka zalika hukumar ta na sa ran a koma aiki a filayen jiragen Aminu Kano da ke garin Kano da babban filin tashi da saukar jiragen saman Fakwakal, da ke garin Choba, a jihar Ribas.

Idan ba ku manta ba a ranar 13 ga watan Maris gwamnatin tarayya ta bada umarnin a rufe duk wani filin tashi da saukar jirgin sama bayan samun rahoton barkewar annobar COVID-19.

Bayan wani zama da hukumar NCAA ta yi a ranar Asabar da ta gabata, gwamnatin tarayya ta fara tunanin dawowa aiki a kasar. Za a fara ne da bude wasu manyan filayen jirgin sama tukun.

KU KARANTA: Mun cafke wani jirgin sama da ya saba dokar tashi - Hadi Sirika

Shugaban NCAA na kasa, Kyaftin Musa Nuhu, ya ce hikimar takaita tashi da saukar jiragen sama a wasu kayyadaddun filaye shi ne rage cinkoson da za a samu da zarar an koma bakin aiki.

Kyaftin Musa Nuhu ya ce sai da su ka tuntubi wakilan kamfanonin jiragen saman da masu lura da saukar jirage kafin su tunkari ma’aikatar harkar jiragen saman kasar da wannan lamari.

“Watakila mu dawo da tashi a cikin gida a filayen jiragen sama hudu ko biyar, kuma mu na sa rai daga baya sai a bude sauran filayen idan abubuwa sun dawo daidai.” Inji shugaban NCAA.

Musa Nuhu ya kara da cewa: “Ba mu so mu yi garaje a lokaci guda, abubuwa su zo su cabe mana. Mu na sa rai nan da ‘yan kwanaki kadan mu cin ma yarjejeniya da jirage na dawowa aiki”

Nuhu ya bayyana cewa gwamnati ta na bukatar kudin shiga, sannan ya nuna zai yi wahala a iya bada tazarar mita biyu da ake bukata domin gujewa yiwuwar kamuwa da cutar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel