ASUU ta dawo tattaunawar janye yajin aiki ko ta ɗanɗana kuɗarta - Ngige

ASUU ta dawo tattaunawar janye yajin aiki ko ta ɗanɗana kuɗarta - Ngige

Ministan kwadago da samar da aikinyi, Chris Ngige ya gargadi kungiyar ASUU ta malaman jami’o’in gwamnati cewa za su ga babu dadi idan ba su dawo an cigaba da tattaunawa ba.

Dr. Chris Ngige ya ce ASUU za ta gamu da matsala muddin ta ki amsa tayin gwamnatin tarayya na komawa zaman da ake yi domin kokarin cin ma matsaya game da dogon yajin aikin.

Chris Ngige ya yi wannan jawabi ne ta bakin mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai, Emmanuel Nzomiwu, ne a ranar 31 ga watan Mayu, 2020.

A cewar Ngige, doka ta haramtawa ma’aikatan gwamnatin tarayya su dumfari NAP ko kuma kotun ma’aikata na NIC, ya ce takaddamar gwamnati da ASUU duk a kan tsarin IPPIS ne.

“Duk wata hujja da ASUU ta bada buge ce. Na gayyaci ‘Yan ASUU taro ta manhajar ZOOM saboda bin sharudan yaki da cutar COVID-19, amma sun ce a'a, dole sai mun gana ido-da-ido.”

KU KARANTA: Abin da ya sa kungyar ASUU ta ke yajin aiki a Najeriya - Farfesa

ASUU ta dawo tattaunawar janye yajin aiki ko ta ɗanɗana kuɗarta - Ngige
Ministoci Chris Ngige, Festus Keyamo da Shugabannin kungiyoyi
Asali: Twitter

“Mu na da dokokin kwadago da matakan raba gardama. Akwai NAP da NIC. Idan na gaji zai kai maganar can. Don haka ya fi masu su zo mu zauna, mu shawo kan matsalar a junanmu."

Ministan ya ce ASUU ba ta da hurumin da za ta fadawa gwamnati yadda za a biya ta. “Muhimmin abu shi ne albashinku su zo maku. Za a biya ku gumin da ku ka yi. Haka ake yi a ko ina”

Ngige ya ce ana asarar haraji daga jami’o’i wanda har kudin da su ka yi gibi su ka taru su ka kai Naira biliyan 800. A game da alawus din malaman, Ngige ya ce za su biya Naira biliyan 25.

Haka zalika ministan kwadagon ya bayyana cewa gwamnati za ta fitar da Naira biliyan 50 domin babbako da sha’anin ilmin jami’o’i, ya ce gwamnatin tarayya har ta fara biyan rabin kudin.

“Gwamnati ta gaza biyan ASUU ragowar Naira biliyan 25 a Oktoban bara. Sai su ka ce mun gaza cika alkawari. Mun yarda za a biyasu alawus dinsu a cikin watan Afrilu da Mayun bana.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel