Bauchi: Manema labarai basu fahimceni ba a kan silar mace-mace - Dr Mohammed

Bauchi: Manema labarai basu fahimceni ba a kan silar mace-mace - Dr Mohammed

Shugaban Hukumar asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na jihar Bauchi, Dr Rilwanu Mohammed ya ce ba a fahimcesa ba a kan rahoton da ya bada na abubuwan da ke kawo mace-macen jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito cewa shugaban ya bayyana cewa zubar da ciki wanda ba kwararru ke yi ba yana daga cikin abinda ke kawo mace-macen jihar.

Kamar yadda ya bayyana, babu alaka tsakanin wannan al'amari da mace-macen da ke faruwa a Azare da sauran kananan hukumomi da ke jihar.

Shugaban yana magana ne a kan mutuwar wasu mata 200 da ya auku a fadin jihar.

Bauchi: Manema labarai basu fahimceni ba a kan silar mace-mace - Dr Mohammed
Bauchi: Manema labarai basu fahimceni ba a kan silar mace-mace - Dr Mohammed Hoto: Naija Home Based
Asali: Twitter

A takardar da cibiyar ta bayyana, jami'in yada labarai, Ibrahim Sani, ya ce kafafen yada labaran basu kyauta ba kuma ba a gane abinda yake nufi ba don magana yayi a kan tazarar iyali.

A yayin bayani a kan matsayar shugaban kungiyar, Sani ya ce "Dr Mohammed yana jaddada wa ne a kan amfanin tazarar iyali wanda yace hakan zai rage yawan mace-macen da ke aukuwa a jihar."

Ya kara da cewa, "Shugaban hukumar bai caccaki wani yanki ba ko kuma magana a kan zubda ciki ga manema labarai."

Hakazalika, wata kungiyar matasa da ke Katagum ta yi barazanar maka shugaban cibiyar a kotu a kan wannan rahoton.

A wata takarda da kungiyar matasan ta bayyana, ta ce "Muna bukatar Dr Rilwanu Mohammed da ya tabbatar mana da ikirarin da yayi ta hanyar bayyana masana lafiyar da ke zubda cikin ko kuma ya fito ya bada hakuri. Idan bai yi daya ba, zai fuskanci fushin hukuma."

A baya mun ji cewa Shugaban hukumar kula da matakin farko na kiwon lafiya a jihar Bauchi, Dr. Rilwanu Mohammad ya bayyana cewa mata fiye da 200 su ka rasa ransu sanadiyyar zub da ciki.

Dr. Rilwanu Mohammad ya ce wadannan mata sun mutu a sakamakon fadawa hannun ruba-ruban likitoci da malaman asibiti. Jaridar The Guardian ta fitar da wannan rahoto.

Rilwanu Mohammad ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’ar da ta gabata lokacin da ya ke tattaunawa da ‘ya ‘yan wata kungiya ta masana kiwon lafiya da ke jihar Bauchi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel