Yadda tsohon gwamnan APC ya dinga biyan kansa alawus din N50m duk bulaguro zuwa Abuja

Yadda tsohon gwamnan APC ya dinga biyan kansa alawus din N50m duk bulaguro zuwa Abuja

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce tsohon gwamnan APC da ya kayar, Mohammed Abubakar, ya dinga karbar alawus na N50m duk lokacin da ya yi bulaguro zuwa Abuja daga Bauchi.

Mohammed ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai domin tattaunawa da shi a yayin da ya cika shekara daya a kan kujerar gwamnan jihar Bauchi.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambaya a kan zargin da jam'iyyar APC a jihar Bauchi ke yi ma sa a kan cewa gwamnatinsa ba ta bin ka'idoji kafin bayar da kwangiloli.

"Ban damu da zuwa Abuja ba. A gwamnatin baya, ta tsohon gwamna Mohammed Abubakar, ana kashe N50m don kawai zuwa Abuja, amma su a wurinsu hakan bin ka'ida ne.

"N50m don kawai an yi bulaguro zuwa Abuja, ya na nan a rubuce, mu na da shaida. Ni ba ma na karbar irin wannan alawus.

"Kamar yadda tsari ya tanada, babban hadimina zai rike miliyan N3m zuwa N5m idan za mu yi tafiya.

"Jama'a aiki su ke bukata, ba za ka iya yi musu aiki ba idan kana karbar N50m duk bulaguro. A bulaguro hudu zuwa Abuja ya kama N200m kenan, ina za a samu kudin da za a yi wa jama'a aiki?.

Yadda tsohon gwamnan APC ya dinga biyan kansa alawus din N50m duk bulaguro zuwa Abuja
Bala Mohammed
Asali: UGC

"Mu na tattalin dukiyar jama'a, ba ma almubazzaranci da ita. Hakan ne ya sa jama'a su ka yarda da ni duk da irin bincike da muzanta da na ke fuskanta a hannun gwamnatin tarayya ta jam'iyyar APC," a cewar gwamnan.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin rundunar NAF 6 da aka kora saboda kisan Alex Badeh

Da ya ke mayar da martani a kan zargin Ali M. Ali, hadimin tsohon gwamnan jihar Bauchi, ya ce gwamnati mai ci na son kawar da hankalin jama'a ne kawai daga gazawarta.

"Ya kamata su daina kokarin dauke hankalin mutane da labaran karya.

"Haka kwanaki su ka ce 'wai' su na bukatar toshuwar gwamnati ta dawo da N1tn. Su na yin hakan ne sakamakon sukar da su ke sha daga jama'ar da su ka zabesu.

"Yanzu kuma sun zo da maganar N50m yayin kowanne bulaguro zuwa Abuja, ta ya ya hankali zai yarda da haka?, a kan wa za a kashe kudin, bayan gwamna a gidan kansa ya ke sauka duk lokacin da ya je Abuja?, wannan zance ne da hankali ba zai dauka ba," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng