Jinjirin da cutar COVID-19 ta harba ya samu lafiya – Gwamnatin Kaduna

Jinjirin da cutar COVID-19 ta harba ya samu lafiya – Gwamnatin Kaduna

- Wani jariri da cutar Coronavirus ta harba a Jihar Kaduna ya warke sarai

- Kwamishinar harkar kiwon lafiya a jihar Kaduna ta ce an sallami jaririn

- A halin yanzu akwai mutane fiye da 70 da ke jinyar Coronavirus a Kaduna

Kwamishinar harkar kiwon lafiya ta jihar Kaduna, Amina Mohammed-Baloni ta ce wani jariri da ya ke jinya a jihar ya warke daga cutar Coronavirus, kuma likitoci sun sallame shi.

Makonni biyu da su ka wuce aka samu wani jariri mai watanni hudu da haihuwa da ya kamu da COVID-19. Mahaifin jaririn ya ziyarci jihar Kano inda ake zargin ya dauko cutar.

A ranar Asabar, 30 ga watan Mayu, 2020, Dr. Amina Mohammed-Baloni ta tabbatar da cewa wannan jariri ya bar gadon asibiti bayan an yi gwaji an gano cewa ya samu lafiya.

Duk da an sallami wannan jinjiri, kwamishinar lafiyar ta ce akwai mutane 76 da yanzu haka su ke kwance a gadon asibiti, su na fama da wannan cuta ta COVID-19 a fadin Kaduna.

KU KARANTA: Masu Coronavirus su na daf da dumfarar mutum 10, 000 a Najeriya

Channels TV ta ce Mohammed-Baloni ta ce a ranar Juma’ar da ta wuce, mutane 76 ake da labarin su na dauke da COVID-19. An sallami mutane 149 da cutar ta kama daga asibiti.

A jihar Kaduna, mutane bakwai ne su ka mutu a sanadiyyar wannan cuta mai hana numfashi. Daga lokacin da annobar ta barke, mutum 232 su ka harbu da COVID-19 a Kaduna.

“Jihar Kaduna ta yi wa mutane kusan 2, 000 gwaji, masu dauke da cutar za su kara yawa saboda karin gwajin cutar da ake yi a wasu wurare.” A cewar Amina Mohammed-Baloni.

Mohammed-Baloni ta ce: “An samu sababbin mutane masu dauke da cutar a mazabu 33 da ke cikin kananan hukumomin Chikun, Giwa, Igabi, Makarfi, Sabon-Gari, Soba, da Zaria.

Sauran kananan hukumomin da aka samu masu dauke da cutar su ne Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu. “Kashi 80% na masu kamuwa da cutar maza ne.” inji kwamsihinar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel