Buhari: NGF ba ta yi na’am da ba bangaren shari’a da Majalisar dokoki gashin kai-ba

Buhari: NGF ba ta yi na’am da ba bangaren shari’a da Majalisar dokoki gashin kai-ba

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta NGF, ba ta amince da ‘yancin tattalin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya damkawa ‘yan majalisar dokoki da bangaren shari’a na jihar ba.

Gwamnonin kasar sun nuna rashin goyon bayan matakin da shugaban kasar ya dauka na rattaba hannu a kan wata doka mai-iko wanda ta ba bangarorin gwamnatin damar cin gashin kai.

Shugaban kungiyar NGF, Dr. Kayode Fayemi ya fadawa jaridar The Nation a boye cewa zai kira taron gaggawa na dukkanin gwamnoni domin duba yadda za a shawo kan wannan lamari.

Kungiyar ta ganin cewa wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka ya sabawa dokar kasa, kuma babu dalilin yin hakan. Kafin nan NGF ta zauna da ministan shari’a, Abubakar Malami.

“Mun zabi shugaban NGF, ya zauna da shugaban kasa da ministan shari’a domin gujewa zuwa kotu gaban alkalai su raba gardama kan abin da sashe na 121 na kudin tsarin mulki ya ce.”

KU KARANTA: Buhari ya sa Majalisar dokoki da bangaren shari'a za su tsaya da kafafunsu

Buhari: NGF ba ta yi na’am da ba bangaren shari’a da Majalisar dokoki gashin kai-ba
Gwamnonin Kaduna, Sokoto da Ekiti Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Jaridar ta rahoto wani gwamnan Arewa maso tsakiya ya na mai wannan jawabi. Gwamnan ya kara da cewa: “Mun fi so mu zauna ayi sulhu, a maimakon ayi fito na fito ana tunkarar juna.”

“Babu dalilin kawo wannan doka ta 10 da shugaban kasa ya rattabawa hannu, kuma sabawa kundin tsarin mulki ne. Ku na ganin yadda AGF ya ke ta kokarin kare dokar.” Inji gwamnan.

“Shugaban NGF ya zauna da shugaban kasa ranar Alhamis, inda ya nuna masa inda EO10 ta sabawa doka. A wani zama da aka yi da Malami, ya yarda dokar ta ci karo da tsarin mulki.”

Ya ce: “Za a sake zama da ministan shari’a da kwamitin NGF wanda su ka hada da gwamnonin jihohin Sokoto, Filato da Ondo. EO10 ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.”

Gwamnan ya ke cewa majalisar dokoki ta bada damar kirkirar asusun hadaka, don haka dokar da shugaban kasa ya kawo rana guda ba za ta iya rusa dokar da ‘yan majalisar jiha su ka yi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel