Jerin sunayen sojojin rundunar NAF 6 da aka kora saboda kisan Alex Badeh
- Kotun rundunar sojoji da ke zamanta a wani sansani rundunar sojojin sama (NAF) ta yankewa wasu dakaru 6 hukuncin zaman gidan yari
- Sojojin da hukuncin ya shafa sun kasance hadimai ma su kare lafiyar marigayi Alex Badeh, tsohon babban rundunar tsaro ta kasa (CDS)
- An kashe marigayi Alex Badeh ta hanyar bude ma sa wuta yayin da ya ke kan hanyarsa ta dawowa gida daga gonarsa a shekarar 2015
Wata babbar kotun sojoji da ke sansanin rundunar sojojin sama (NAF) a Abuja ta tura wasu sojojin rundunar su 6 zuwa gidan yari.
Sojojin da hukuncin ya shafa su na aiki ne tare da tsohon babban hafsan rundunar tsaro ta kasa (CDS), marigayi Alex Badeh.
An kashe Badeh ta hanyar bude ma sa wuta yayin da ya ke kan hanyarsa ta dawowa gida daga gonarsa da ke kan titi Abuja zuwa Keffi.
Badeh ya shugabanci rundunar sojojin NAF kafin daga bisani ya zama CDS daga watan Janairu na shekarar 2014 zuwa watan Yuli na shekarar 2015.

Asali: Twitter
A wani jawabi da Ibikunle Daramola, darektan hulda da jama'a na rundunar NAF, ya fitar ranar Asabar, ya ce an zartar da hukuncin ne a kan sojojin saboda kasancewarsu wadanda ya kamata su bawa Badeh tsaro.
Sai dai, jawabin bai nuna tsawon wa'adin da dakarun sojin za su yi a gidan yari ba.
DUBA WANNAN: Cutar korona ta hallaka babban Limami, Sheikh Ahmad Abubakar
Dakarun da hukuncin ya shafa sune kamar haka; Tom Gwani, Amu David, Philemon Degema, Sabo Simon, Mukhtar Abdullahi da Alfred Alexander.
"An yankewa jami'an NAF 6 hukuncin dauri a gidan yari, kotun sojoji ta GCM da ke sansanin NAF na Bill Clinton Drive, Abuja, ita ce ta yanke wannan hukunci," a cewarsa.
Daramola ya kara da cewa, "hukuncin ya hau kan sojojin ne saboda kasancewarsu hadimai ma su kare lafiyar marigayi Badeh."
A cewar Daramola, alkalin kotun, Air Commodore David Aluku, ya samu sojojin da laifuka da su ka hada da gazawa, sakaci da aiki, bayar da bayanan karya da sauransu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng