Satar N449.5m: Hukumar EFCC ta kama babban kwamandan yan bangan jahar Benuwe

Satar N449.5m: Hukumar EFCC ta kama babban kwamandan yan bangan jahar Benuwe

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kama kwamandan yan bangan jahar Benue, George Mbessey kan zarginsa da satar naira miliyan 449.5.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe mutane 13 a wani sabon hari da suka kai jahar Katsina

Daily Trust ta ruwaito jami’an EFCC sun kama George ne a garin Makurdi a ranar Laraba, 28 ga watan Mayu bayan samun korafi a kansa inda zake zarginsa da bindiga da kudin kungiyar.

Jami'in watsa labaru na hukumar EFCC, Dele Oyewale ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, inda yace sun samu korafekorafe ne daga wasun yan kishin jahar.

Dele yace korafin da suka samu shi ne kungiyar yan bangan tana samun kudi naira miliyan 20 a duk wata daga hukumar dake kula da kananan hukumomi da masarautun gargajiya.

Satar N449.5m: Hukumar EFCC ta kama babban kwamanda yan bangan jahar Benuwe
Mbessey Hoto: Shafin EFCC
Asali: Facebook

Hakazalika hukumar EFCC ta ce hukumar dake kula da kananan hukumomi da masarautun gargajiya tana antaya kudin ne kai tsaye a asusun bankin hukumar kungiyar yan bangan.

A cewar Dele, a tsakanin watan Oktoban shekarar 2018 zuwa Mayun 2020, kungiyar yan bangan ta samu kimanin naira miliyan 449.5 ta hanyar amfani da asusun bankinsa ban a hukumar ba.

EFCC ta bayyana hakan a matsayin yi ma doka karan tsaye, amma ta ce Mbessey yana basu bayanan da suka kamata, kuma za su gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.

A wani labarin kuma, Hukumar yaki da rashawa da makamanta laifuka, ICPC ta sanar da fara binciken a kan zargin rashawa da satar kudaden tallafin Coronavirus da aka tara ma gwamnati.

Daraktan ayyuka na hukumar, Akeem Lawal ne ya bayyana haka yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana ta bidiyon kallo kallo da aka yi a ranar Alhamis, 28 ga watan Mayu.

Taken taron shi ne: “COVID-19, gudanar da kudaden tallafi tare da sanya idanu a kan su”, inda yace suna binciken zargin almundahana a hukumomin gwamnati wajen rabon tallafin hatsi.

Sauran sun hada da zargin rashawa wajen sayo kayan tallafin COVID-19, kudaden zirga zirga da kuma kudaden da aka kashe wajen wayar da kawunan jama’a game da cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel