Kaduna: An sako limamin da ya ja sallar Juma'a a Zaria

Kaduna: An sako limamin da ya ja sallar Juma'a a Zaria

An sako Limamin da jami'an tsaro suka kama a kan jan sallar Juma'a a garin Zaria bayan kwanaki hudu da ya kwashe a wurin 'yan sanda.

A yayin da aka tuntubi limamin a yau Juma'a, Malam Muhammad Tukur ya ki yin tsokaci don ya ce Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa iqamatis Sunnah ta Zaria ta umarcesa da yayi shiru.

Amma kuma, ya tabbatar da cewa an sako shi a ranar Laraba bayan an kai shi gaban kotu.

Bayan kama Idris da aka yi a ranar Juma'a, 22 ga watan Mayu, Malam Sani Yakubu, shugaban kungiyar JIBWIS reshen Zaria ya tabbatar wa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin.

Daya daga cikin mamun ya tabbatar da cewa sun yi sallar Juma'a din ne saboda watan Ramadana mai alfarma ne.

Kaduna: An sako limamin da ya ja sallar Juma'a a Zaria
Kaduna: An sako limamin da ya ja sallar Juma'a a Zaria Hoto: Channels Television
Asali: UGC

Ya kara da cewa: "Saboda bamu yi sallar Juma'a ba na makonni tara, mun bukaci Malam Tukur da ya ja mu sallar Juma'a a kalla ko ta karshe ce a watan Ramadana. Gaskiya ba shi ya shirya sallar ba.

"An rokesa ne kuma ya amince. Mu mutane ne masu son zaman lafiya don haka ne yasa muke biye wa dokokin gwamnati. Amma ba za mu zuba ido ana wulakanta malamanmu ba."

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga: Tambuwal zai shiga ganawa da shugaba Buhari

Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta zirga-zirga tare da hana dukkan wuraren bauta budewa don dakile yaduwar annobar Coronavirus a jihar.

A wani labarin, bayan rufe Masallatai na sama da watanni biyu, ma'aikatar al'amuran addinin Musulunci ta Saudiyya ta yi kira ga ma'aikatanta da su fara gyara da tsaftace manya da kananan Masallatai sama da 90,000 a masarautar.

Za a bude Masallatan ne a ranar Lahadi mai zuwa amma banda Masallatan garin Makkah a wannan budewar.

Ma'aikatar na yakin wayar da kai a kafafen yada labarai, Talabijin, rediyo, jaridu da sauran kafafen yada labarai. Ana wannan wayar da kan ne don kiyaye hanyoyin yaduwar cutar ko bayan budewar Masallatai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel