COVID-19: Za a fara turawa jama'a tallafin kudi don rage radadi a Legas

COVID-19: Za a fara turawa jama'a tallafin kudi don rage radadi a Legas

Gwamnatin jihar Legas ta amince da fara tura wa mabukatan jihar tallafin kudi na rage radadi karkashin shirin 'National Cash Transfer Programme'.

Kwamishinan kirkiro arziki da aikin yi, Yetunde Arobieke ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis a garin Legas yayin bada bayanin abubuwan da suka faru a ma'aikatarta na tsawo shekarar daya karkashin mulkin Gwamna Babajide Sanwo-Olu.

Ta ce nan da makonni kadan za a fara biyan kashi na farko na mutanen da za su amfana da shirin.

COVID-19: Za a fara tura wa jama'a tallafin kudi don rage radadi a Legas
COVID-19: Za a fara tura wa jama'a tallafin kudi don rage radadi a Legas Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Ta ce a halin yanzu akwai mutum 8,147 mabukata a kananan hukumomi shida da kuma gunduma 40 da za su amfana da shirin.

Ta ce za a biya naira dubu biyar-biyar ga mabukatan. Wadanda za su amfana din na daga kananan hukumomin Amuwo Odofin, Apapa, Badagry, Epe, Ibeju Lekki da tsibirin Legas.

Ta kara da cewa ana ci gaba da bincikowa tare da gano mabukata a sauran kananan hukumomi kuma za a fara mika musu tallafin ne bayan an kammala.

Ta ce don tabbatar da aikin ya tafi yadda ake so, ma'aikatarta tare da hadin guiwar ofishin Cash Transfer na kasa da ke Abuja sun shirya taron horarwa ga masu tura kudin.

Arobieke ta ce gwamnati na kokarin samar da hanyar koyar da matasa ayyukan dogaro da kai don hakan ya zama hanyar samun aikin yi garesu.

Ta ce bangaren zai horar da matasa ne wajen sarrafa fata da kuma kiwon kifi don assasa ci gaba a bangaren kiwo.

KU KARANTA KUMA: Katsina: Masari ya bada umarnin bude Majami'u da Masallatai, ya kafa sharadi

A wani labarin kuma, fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce a shekaru biyar da suka gabata, ta taba rayuwar 'yan Najeriya a fanni daban-daban.

An rantsar da Buhari a karo na biyu a ranar 29 ga watan Mayun 2020. A yau Juma'a ne yake cika shekaru biyar cif a kan karagar mulkin kasar nan.

Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya saki wasu jawabai a kan nasarorin da shugaban kasar ya samu a cikin shekaru biyar, duk da kuwa yace tagomashin damokaradiyyar bai riga ya iso duka ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel