Buhari ya yi garambawul a rundunar 'yan sanda, ya kirkiri sabbin kwamand 5

Buhari ya yi garambawul a rundunar 'yan sanda, ya kirkiri sabbin kwamand 5

Kwanan nan sashen binciken sirri na rundunar 'yan sanda (FIB) zai fara cin gashin kansa, saboda za a cire shi daga karkashin bangaren binciken manyan laifuka (FCID).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya rattabawa hannu kafin aikawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya.

Ya ce za a nada babban mataimakin babban sifeton 'yan sanda da zai jagoranci sashen FIB da zarar an dauke shi daga karkashin sashen FCID.

"Hakan zai bayar da damar tattara hankali wajen gudanar da binciken sirri domin inganta aikin dan sanda da samun saukin fuskantar kalubalen barazanar da aiyukan ta'addanci ke yi wa tsaron kasa," a cewar IGP.

A cewarsa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi amfani da matsayinsa wajen yin garambawul tare da kawo sauye - sauye a rundunar 'yan sanda.

Buhari ya yi garambawul a rundunar 'yan sanda, ya kirkiri sabbin kwamand 5
Buhari ya yi garambawul a rundunar 'yan sanda, ya kirkiri sabbin kwamand 5
Asali: Facebook

Adamu ya kara da cewa, bisa sabbin sauye - sauyen da shugaba Buhari ya yi, yanzu haka rundunar 'yan sanda ta na da kwamand guda takwas.

"Domin kawo 'yan sanda kusa da jama'a, shugaba Buhari ya amince da kirkirar sabbin kwamand na 'yan sanda guda biyar," a cewarsa.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun yi wa mutane 13 yankan rago, sun kashe fiye da 60 a Sokoto

Sabbin kwamand din da aka kirkira sune kamar haka; Awka kwamand; wanda zai hada da jihohin Enugu, Anambra da Ebonyi, kwamand din Akure; wanda zai hada da jihohin Ondo da Ekiti.

Sai kwamand din Yenagoa; wanda zai hada da jihohin Bayelsa da Ribas, kwamand din Maiduguri; wanda zai hada da jihohin Yobe da Borno da kwamand din Katsina; wanda zai hada da jihohin Katsina da Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng