Kabilar Hausa: Kabilar da ta fi kowacce yawa a nahiyar Afrika

Kabilar Hausa: Kabilar da ta fi kowacce yawa a nahiyar Afrika

- Kabilar Hausa ce ta bayyana a matsayin kabilar da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afrika

- Ana yin yaren ne a kasashen Najeriya, Nijar, Cahdi, jamhuriyar Benin, Kamaru, Togo da sauransu

- Yaren da ke da jama’a miliyan 78 ne ya zamo na biyu da ake yi a yankin

Akwai abubuwa masu tarin bada mamaki game da kabilar Hausa. Kabilar na da mutane da suka kai miliyan 78 a fadin nahiyar Afrika.

Hakan ne yasa ta zamo kabila mafi yawan mutane a fadin nahiyar Afrika.

Kamar yadda aka gano, yaren Hausa ne yaren da aka fi yi kuma mafi dadewa a cikin yankin mutane miliyan 120.

Masu yin yaren na nan dankam a kasashen Najeriya, Nijar, Chadi, jamhuriyar Benin, Kamaru, Togo, jamhuriyar Afrika ta tsakiya, Ghana, Sudan, Eritrea, Guinea, Gabon, Senegal da Gambia.

Kamar yadda Africa Facts Zone ta wallafa a shafinta na twitter, ta ce “Kabilar Hauce ce kabila mafi girma a Afrika tare da mutane miliyan 78. Yaren Hausa ne yare na biyu da aka fi yi a Afrika tare da kimanin mutane miliyan 120 da ke yi ta a Najeriya, Chadi, Benin, Kamaru, Togo, CAR, Ghana, Eritrea, Equatorial Guinea, Gabon, Senegal, Gambia da ma fadin duniya.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace rijistar jam'iyyun siyasa 74 (Sunayen masu rijista)

A wani labari kuma, mun ji cewa adadin mutanen da 'yan bindiga su ka kashe yayin harin da su ka kai ranar Laraba a jihar Sokoto ya tashi zuwa 75.

'Yan bindigar sun kashe mutane 25 a kauyen Garki, yayin da suka yi wa mutane 13 yankan rago a kauyen Dan Aduwa, kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Kazalika, 'yan bindigar sun kashe mutane 6 a kauyen Kutama tare da yin garkuwa da wani mutum guda, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

An samu gawar mutane 25 a kauyen Kuzari a yayin da aka samu gawar mutane biyar, da suka hada da yara, a kauyen Masawa. An garzaya da wadanda su ka samu raunuka zuwa babban asibitin Sabon Birni.

SaharaReporters ta rawaito cewa har yanzu ana cigaba da binne gawarwakin mutanen da 'yan bindigar su ka kashe yayin munanan hare - haren da su ka kai jiya, Laraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel