'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 70 a mummunan harin da su kai Sokoto

'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 70 a mummunan harin da su kai Sokoto

Adadin mutanen da 'yan bindiga su ka kashe yayin harin da su ka kai ranar Laraba a jihar Sokoto ya tashi zuwa 75.

'Yan bindigar sun kashe mutane 25 a kauyen Garki, yayin da suka yi wa mutane 13 yankan rago a kauyen Dan Aduwa, kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Kazalika, 'yan bindigar sun kashe mutane 6 a kauyen Kutama tare da yin garkuwa da wani mutum guda, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito.

An samu gawar mutane 25 a kauyen Kuzari a yayin da aka samu gawar mutane biyar, da suka hada da yara, a kauyen Masawa.

An garzaya da wadanda su ka samu raunuka zuwa babban asibitin Sabon Birni.

SaharaReporters ta rawaito cewa har yanzu ana cigaba da binne gawarwakin mutanen da 'yan bindigar su ka kashe yayin munanan hare - haren da su ka kai jiya, Laraba.

'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 70 a mummunan harin da su kai Sokoto
'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 70 a mummunan harin da su kai Sokoto Hoto: SaharaReporters
Asali: UGC

'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 70 a mummunan harin da su kai Sokoto
'Yan bindiga sun kashe mutane fiye da 70 a mummunan harin da su kai Sokoto Hoto: SaharaReporters
Asali: UGC

Mazaunann kauyukan da hare - haren da su ka shafa basu san halin da 'yan uwansu da ke ciki ba a halin yanzu.

DUBA WANNAN: Korona ta hallaka mutane uku a Kano, an kama almajirai fiye da 1000

Wasu daga cikin mazauna kauyukan sun yi zargin cewa makiyaya ne su ka kai hari domin hana manoma gyara gonakinsu domin shirin fara noma a yayin da damina ta fara faduwa a arewacin Najeriya.

Ganau ba jiyau ba, sun ce maharan sun dauki tsawon sa'o'i suna ruwan wuta a kauyukan ba tare da kowa ya tunkaresu ba.

Hakazalika, wata mata da 'yan bindiga uku sun mutu a cikin wani harin da suka kai karamar hukumar Gwadabawa ta jihar.

Wani jami'in da ya samu zuwa inda al'amarin ya faru, ya sanar da BBC cewa, da misalin karfe uku zuwa biyar na yammacin Laraba ne suka samu labarin cewa mutane sun taso da babura kusan 100 daga daji.

Mutanen sun taho ne daga dajin da ke kusa da Issa sannan sun nufi kauyukan.

A cewarsa, "Koda muka samu labari, mun je mun sanar da jami'an tsaro abinda ke faruwa. Daga nan sai mutanen suka isa garin Garki zuwa garin Dan Adu'a."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel