Wakar da ta sa Ministan Labarai, Lai Mohammed, ya ba da umarnin a kama dan jarida, Jolayemi

Wakar da ta sa Ministan Labarai, Lai Mohammed, ya ba da umarnin a kama dan jarida, Jolayemi

A yau mun kawo muku baitocin wakar da ta sanya Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, ya ba da umarnin cafke wa tare da tsare wani dan jarida na jihar Kwara, Rotimi Jolayemi.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, Ministan ya ba da umarnin dakume dan jaridar kuma mawakin na jihar Kwara da ya shahara da sunan Oba Akewi.

Gabanin dan jaridar ya mika kansa ga jami'an tsaro na 'yan sanda, Ministan ya ba da umarni a cafke matarsa, Mrs Dorcas Jolayemi da wasu 'yan uwansa maza biyu; John da Joseph, wadanda su ma sun kasance 'yan jarida.

Sai dai tun bayan da jaridar ya mika kansa zuwa babban ofishin 'yan sanda da ke birnin Ilorin na jihar Kwara, a ranar 6 ga watan Mayu, har yanzu yana tsare ana gallaza masa azaba kamar yadda Ministan ya ba da umarni.

Jolayemi wanda ya jagoranci wani shiri mai taken ‘Bi aye se ri’ da aka yada cikin harshen Yarbanci, ya fada hannun jami’an tsaro ne bayan ya rera wata waka ta cin mutunci da sukar ministan labarai da al'adun kasar.

Da ta ke martani dangane da wannan lamari da ta misalta a matsayin keta haddin bil Adama, kungiyar Amnesty International cikin wani sako da ta wallafa a ranar Talata kan shafinta na Twitter, ta ce cafke dan jaridar ya saba wa shari'a.

Kungiyar mai rajin kare hakkin bil Adama, ta bukaci rundunar 'yan sandan Najeriya ta gaggauta sakin dan jaridar da ta kama wanda a yanzu ya shafe tsawon makonni uku ba tare da ya shaki isakar 'yanci ba.

Saurari baitocin wakar kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta wallafa a shafinta:

KARANTA KUMA: Ranar 8 ga watan Yuni: Gwamnatin Gombe ta yi gargadi a kan bude makarantu

Ga kuma fassarar wakar cikin harshen Hausa a gaggauce:

"Haihuwar da irin Lai Mohammed ba komai bane face babbar asara"

"Sau da dama ya yi wa mutane karya, kuma ya sayar da kasar nan ta dabarunsa na karya"

"Mutumin ya yi karairayi da har ta kai matakin da babu sauran wata karya a jihar Kwara"

"Ga mutanen da suke ganin Lai Mohammed a matsayin wani mai rinjayen tasiri, ku na ganin Lai lafiya kalau yake kuwa"

"Lai ba shi da banbanci da dabba"

"Ya kamata a ce tun tuni ya dade a daure"

"Duk mun san tarihin rayuwar Baba Saraki a jihar Kwara"

"Mun samu labarin yadda Barawon ya rika cin moriya a kansa"

"MAKARYACI!"

"Ya bige da sata da yaudara mu"

"Duk bayan shekara hudu..."

"Sai ya yi shelar ya na son tsayawa takarar kujerar Gwamnan jihar Kwara, ko ba haka bane?"

"Mazaunan Ekiti, Kwara da Igbomina, za su ce Lai na su ne, a ba shi damar ya yi takara, a goyi bayansa da kuri'u"

"Da zarar zabe ya matso..."

"Bayan dan fashi da makamin ya karbi kudi a hannun Baba Saraki"

"Sai kuma ya ce ya janye takara"

"Ko me yasa! Shin Lai ko dai an yi maka wankan jego ne da ruwan karya?

"Ko an yi goyon ka da zanin karya ne, ina da tabbaci a kan haka"

"Ya kamata a ce sunan ka (IROLABI) ma'ana mun haifi makaryaci"

"IGOGBEMI shi ne sunan da ya dace da kai"

"Ko da a ce ana kiran ka da sunan makaryaci"

"Ko wa ya san cewa makaryaci shi ne wanda ya ke da dabi'a ta karya"

"Dubi adadin karairayin da wannan Mahaukacin ya shirga tun bayan barkewar annobar cutar COVID-19"

"An faman yunwa a kasar amma Mahaukacin ya ce an rabawa 'yan kasa Naira biliyan 100"

"Wane gidan ka ba wa, ko kuma dai gidan Mahaifinka ka kai kudin wanda yake Oro, domin ni na kasa fahimta"

"Da Lai Mohammed da Ministan Agaji da Ci gaban Al'umma"

"Madam Umar Sadiyat Faruq, farkar Buhari kuma jagorar barayi"

"Irin cutarwar da ta ke yi wa ma'aikatan shirin N-Power ta wuce misali"

"Da dimuwar da annobar korona ta haddasa"

"Ma'aikatan N-Power ba su da kudi, ba su da wata hanyar samu, kuma ba a biya su albashinsu ba, Ina mamaki"

"Su na binta bashin albashin watanni biyu zuwa uku"

"A halin yanzu ma dai ba su samu albashin watanni uku ba"

"Wannan lamari ya kai intaha, amma kuma Mahaukaciyar ba ta jin tsoron Allah"

"Ba mamaki shi yasa Majalisar Dokoki ta Tarayya ta titsiye ta a kan sai ta fadi yadda aka batar da kudin ba da tallafin rage radadin annobar korona"

"Ta ce an kashe Naira Tiriliyan 1, Majalisar Dokoki ta Tarayya ta bukaci ta yi bayanin yadda aka kashe kudin"

"Ta ce duk hanyoyin da aka bi wajen kashe kudin, shaidar ta na nan a rubuce a hannun Akanta Janar na kasa, Alhaji Ahmed Idris"

"Ba za ku yi mamakin yadda gobara ta tashi a ofishin Akanta Janar ba washe gari da yin wannan magana ba"

"Idris ya ce kudin da shaidar yadda aka kashe kudin duk sun kone a gobara"

"Dukkan ku ba ku yi sa'ar rayuwa ta gari ba", a nan wakar ta kare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel