Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace rijistar jam'iyyun siyasa 74 (Sunayen masu rijista)

Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace rijistar jam'iyyun siyasa 74 (Sunayen masu rijista)

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta jaddada ikon hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na kwace rijistar wasu jam’iyyun siyasa wadanda suka ki biyayya ga tanadin sashi na 225 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999.

Mai shari’a Taiwo O. Taiwo ya bada wannan hukuncin bayan jam’iyyar National Unity Party, daya daga cikin jam’iyyun da aka kwace wa rijista ta kai kara kotu.

A don haka ne jam’iyyar NNP din ta tashi daga jam’iyyar siyasa a Najeriya sakamakon shigarta cikin jerin jam’iyyu 74 na kasar nan da basu bi tsarin dokar kasa ba yayin rijista.

Idan za a tuna, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu, a watan Fabrairu, ya sanar da kwace rijistar wasu jam’iyyu 74 cikin 91 na kasar nan.

Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace rijistar jam'iyyun siyasa 74 (Sunayen masu rijista)
Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace rijistar jam'iyyun siyasa 74 (Sunayen masu rijista)
Asali: UGC

Da wannan ci gaban, kasar nan tana da jam’iyyun siyasa 18 masu rijista kenan.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Sharudda 4 da FG ta bai wa CAN da NSCIA don bude wuraren bauta

Jam’iyyun da suka tsallake rijiya da baya kuma ba a kwace rijistar ba suna hada da:

1. Accord Party (AP)

2. Action Alliance (AA)

3. African Action Congress (AAC)

4. African Democratic Congress (ADC)

5. African Democratic Party (ADP)

6. All Progressives Congress (APC)

7. All Progressives Grand Alliance (APGA)

8. Allied Peoples Movement (APM)

9. Labour Party (LP)

10. New Nigeria Peoples Party (NNPP)

11. National Rescue Movement (NRM)

12. Peoples Democratic Party (PDP)

13. Peoples Redemption Party (PRP)

14. Social Democratic Party (SDP)

15. Young Progressive Party (YPP)

16. Zenith Labour Party (ZLP).

Amma kuma, Yakubu ya ce daya daga cikin jam’iyyun mai suna Action Peoples Party (APP), ta maka INEC a kotu don haka tana nan da rijistarta har zuwa lokacin da za a ji karar.

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya fito ya na cewa jam’iyyar PDP ba ta lale maraba da dawowar tsohon shugaban jam’iyyar APC, Injiniya Segun Oni.

Mista Ayodele Fayose ya bayyana Segun Oni da mutumin da bai da nauyi a siyasa, don haka ya nuna rashin goyon bayansa ga sauya shekar ‘dan siyasar da ya mulki Ekiti.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel