Yajin aikin: Bayin Allah sun shiga matsala bayan Gwamnan Kaduna ya rage albashin Likitoci

Yajin aikin: Bayin Allah sun shiga matsala bayan Gwamnan Kaduna ya rage albashin Likitoci

Jaridar Daily Trust ta ce ana kin karbar marasa lafiya a asibitocin gwamnatin jihar Kaduna, a sakamakon yajin aikin da kungiyar malaman lafiya su ka shiga a makon da ya wuce.

Kungiyar malaman lafiya na jihar Kaduna sun tafi yajin aiki a ranar Juma’a. Ma’aikatan za su yi kwanaki bakwai ba su taba mara lafiya domin jan-kunnen gwamnatin Mal. Nasir El-Rufai.

Ma’aikatan lafiya na jihar Kaduna sun bukaci gwamna Nasir El-Rufai ya dawo masu da 25% na albashinsu da ya zaftare cikin watannin Afrilu da Mayu, sannan a kawo masu kayan aiki.

Rahoton ya nuna ma’aikatan su na kukan rashin kayan kariyar aiki na PPE wanda ake amfani da su a daidai wannan lokaci da ake fama da annobar cutar Coronavirus a kasashen Duniya.

Duk da barazanar da gwamnatin Kaduna ta yi, malaman kiwon lafiya sun tafi yajin aiki, kuma sun bayyana cewa idan har ba a biya masu bukatunsu ba, za su janye kafa sai baba ta gani

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna ya tare hanyar Kano domin hana Jama'a shigowa

Yajin aikin: Bayin Allah sun shiga matsala bayan Gwamnan Kaduna ya rage albashin Likitoci
Gwamna Nasir El-Rufa. Hoto: Twitter
Asali: Twitter

Gwamnatin jihar Kaduna ta na kare matakin da ta dauka na rage albashi, ta ce wannan ragi ya shafi duk wani ma’aikacin gwamnatin jihar da ke karbar kudin da ya haura N50, 000 a wata.

Wani ‘dan jarida wanda ya ziyarci wasu asibitocin gwamnati a Kaduna ya ce ma’aikata su na zuwa ofis amma ba su aiki. An hangi ma’aikatan ne su na hira a karkashin bishiyar magwaro.

A wani asibitin jihar ba a samu kowane maras lafiya da ke kwance ba. Likitocin sun sallami dukkanin wadanda aka kwantar su na jinya a gadajen da ke sashen mata da maza na asibitin.

Ana kora marasa lafiya ko masu bukatar kula da su ka ziyarci asibitocin gwamnatin jihar. Akwai wata mai juna biyu da aka ki karbarta a asibiti da ke cikin unguwar Muazu a birnin Kaduna.

Rahoton jaridar ya nuna cewa ana zama tsakanin ma’aikatar lafiya da shugabannin asibitocin domin ganin cewa ma’aikata sun koma bakin aiki. Kawo yanzu ba a janye wannan yaji ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel