COVID-19: Sharudda 4 da FG ta bai wa CAN da NSCIA don bude wuraren bauta

COVID-19: Sharudda 4 da FG ta bai wa CAN da NSCIA don bude wuraren bauta

- Akwai tsammanin dage dokar hana tarukan addinai nan kusa bayan taron da PTF tayi da shugabannin kungiyoyin addinai

- A karshen taron, sun amince da sabbin tsarika da za a kiyaye a cibiyoyin bauta na fadin kasar nan

- Daga cikin manyan sharuddan, akwai tilascin amfani da takunkumin fuska da wanke hannu ga masu bauta

Akwai tunanin cewa hana zuwa wuraren bauta a fadin kasar nan sakamakon annobar Coronavirus za a dage ta babu dadewa.

Wannan hasashen ya fara ne bayan taron da kungiyar kiristoci ta kasa, majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci suka yi a kwamitin yaki da cutar coronavirus ta kasa.

Kamar yadda rahoton jaridar The Nation ta wallafa, hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasa sun halarci taron da aka yi tsakanin kwamitin da kungiyoyin a ranar Talata, 26 ga watan Mayu don cimma matsayar bude wuraren bauta.

COVID-19: Sharudda 4 da FG ta bai wa CAN da NSCIA don bude wuraren bauta
COVID-19: Sharudda 4 da FG ta bai wa CAN da NSCIA don bude wuraren bauta Hoto: The Cable
Asali: UGC

Kafin taron kungiyoyin, akwai tsananin matsi ga gwamnati a kan bude wuraren bauta duk da kuwa hauhawar yawan masu dauke da cutar coronavirus a Najeriya.

Akwai yuwuwar nan babu dadewa za a bude wuraren bauta bayan shugabannin kungiyoyin addinai ta yi tark da PTF.

Amma a taron, an amince cewa a bude cibiyoyin addinai amma a karkashin tsauraran matakai na gujewa yaduwar muguwar cutar.

Shugaban kungiyar kiristoci ta kasa (CAN), Rabaren Samson Ayokunle, ya tabbatar da wannan ci gaban.

Ya kara da cewa, za a samar da jami'an tsaro don tabbatar da jama'a sun bi wadannan dokokin. Za a fara da yi wa wuraren bautar feshi. Ga dokokin:

1. Dole ne wuraren bauta su samar da sinadarin kashe kwayoyin cuta, ruwa da sabulu don tsaftace hannu.

2. Dole ne masu bauta su yi amfani da takunkumin fuska bayan wanke hannuwa.

3. Dole ne tsarin zama ya kasance na nesa-nesa da juna a kalla mita daya tsakanin masu bauta.

4. Musabaha tare da rungumar juna dole a gujesu a yayin ko bayan kammala bauta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da shugaban CAN

A gefe guda, gwamnatin jihar Kogi ta ce babu wani mahaluki da ya kamu da cutar COVID-19 da aka fi sani da korona a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel