An aikawa hukuma ‘magungunan gargajiyar COVID-19’ domin bincike - PTF

An aikawa hukuma ‘magungunan gargajiyar COVID-19’ domin bincike - PTF

Gwamnatin tarayya ta ce ta zabi wasu daga cikin magungunan da ake ikirarin an hada domin maganin cutar COVID-19. An kirkiro wadannan magunguna ne daga itatuwa.

A ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2020, shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da Coronavirus, Boss Mustapha, ya shaida cewa sun zabi wasu magunguna uku.

Boss Mustapha ya ce sun aikawa hukumomin da ke da alhakin gudanar da bincike game da tasirin magugunan domin su gano ko za su yi aiki wajen warkar da COVID-19.

Mustapha wanda shi ne sakataren gwamnatin tarayya ya bayyanawa ‘yan jarida wannan a lokacin da ya zanta da manema labarai da yawun bakin kwamitin na PTF a garin Abuja.

Ma’aikatar lafiya ce ta fara tantance tasirin magungunan gargajiyar. Ma’aikatar ta yi aiki da kwararru da masu nazari da bincike kamar yadda shugaban kwamitin ya fada.

KU KARANTA: Bayan wata da watanni, COVID-19 ta shiga Jihar Kogi

An aikawa hukuma ‘magungunan gargajiyar COVID-19’ domin bincike - PTF
Ana neman maganin gargajiyar COVID-19 a Najeriya
Asali: Depositphotos

“An dauki matakin a zauna da masu bincike ne bayan ganin mace-macen da aka yi a Kano da wasu wurare. Abin da ya faru ya yi sanadiyyar kaddamar da binciken.” Inji Boss.

Ya ce: “Domin karfafa binciken COVID-19 a gida, ma’aikatar lafiya ta yi wata ganawa ta yanar gizo da wasu masana da masu bincike da su ke da’awar sun gano maganin Coronavirus."

“Daga cikin tarin ikirarin da aka yi, magunguna uku ne mu ka samu sun cancanci a mikasu gaba ga hukuma domin a kara gudanar da bincike a kansu.” Inji kwamitin shugaban kasar.

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin taimakawa masu irin wannan bincike domin kawo karshen annobar COVID-19. Bankin CBN da PTF ne za su bada gudumuwar kudin binciken.

A dalilin haka ne Boss Mustapha ya kalubalanci masana su tashi tsaye wajen gano maganin cutar. Haka zalika ana binciken kayan aikin da wasu masu fasaha su ka kirkiro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel