Lantarki: Buhari ya amince da fitar da makudan kudi domin fara aikin hadin gwuiwa da SIEMEN

Lantarki: Buhari ya amince da fitar da makudan kudi domin fara aikin hadin gwuiwa da SIEMEN

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sakin kunshin kudi, a karon farko, domin fara aikin samar da wutar lantarki da aka kulla yarjejeniyarsa da kamfanin SIEMENS.

Tun a cikin shekarar 2019 shugaban kasa ya rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar yin aiki tare da kamfanin Siemens domin kara adadin karfin wutar lantarkin kasa da megawat 7,000 zuwa shekarar 2021.

A jerin wasu sakonni da fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na tuwita a ranar Laraba, shugaba Buhari ya bukaci ma'aikatar lantarki da ma'aikatar kudi su kammala dukkan wani shiri domin fara gudanar da aikin.

Buhari ya ce burinsa shine samar da wutar lantarki a kasa domin amfanin gidaje da kamfanoni.

"Shugaban kasa ya bawa ma'aikatar lanatarki, ma'aikatar kudi da sashen kula da aiyuka (BPE) umarnin su kammala dukkan wani shiri tare da samar da kudi domin fara aikin kara karfin wutar lantarkin kasa, wacce aka kulla da kamfanin Siemens AG," a cewar sakon fadar shugaban kasa.

Lantarki: Buhari ya amince da fitar da makudan kudi domin fara aikin hadin gwuiwa da SIEMEN
Buhari
Asali: UGC

"Za ai aikin ne a karkashin shirin shugaban kasa na samar da wutar lantarki (PPI), wanda gwamnatin Najeriya da gwamnatin kasar Jamus za su dauki nauyinsa. Kamfanin Siemens AG na Jamus ne zai yi aikin.

"A karkashin shirin PPI, gwamnatin Najeriya za ta wakilci kamfanonin raba hasken wutar lantarki da sauran ma su ruwa da tsaki wajen saka hannun jari a bangaren ingantawa tare da zamanantar da raba wutar lantarki," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

DUBA WANNAN: Hadarin Daji: An kashe 'yan bindiga fiye da 30 a Zamfara

A cewar sanarwar, za a kashe kudin aikin ne daki - daki a karkashin wasu sharuda na bayar da bashi da biya.

A bisa karkashin tsarin ne shugaba Buhari ya amince da fara fitar da kunshin farko na kudin da za a kashe kafin kammala aikin.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa babban manufar shirin PPI shine kara karfin wutar lantarki da ake da ita a cikin kasa tare da zamanantar da rarrabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel