Da duminsa: Trump ya yi barazanar rufe dandalin sada zumunta

Da duminsa: Trump ya yi barazanar rufe dandalin sada zumunta

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar rufe dandalin sada zumunta bayan manhajar sada zumunta ta tuwita ta saka matakan tsefe kalamansa da ya ke wallafawa a shafinsu.

Jama'a da dama sun soki manhajar tuwita a kan barin shugabanni su na yin amfani da dandalinsu wajen yada maganganun da basu da tushe.

Sabon tsarin da tuwita ta bullo da shi ya fusata Trump, lamarin da ya sa ya bayyana hakan a matsayin salon zamba.

Manhajar tuwita ta tona asirin wani sako da Trump ya wallafa ta hanyar saka wani bayani na gaskiya a kan sakonsa na asali da ya wallafa, wanda kuma ba daidai ya ke ba.

A wani sako da ya wallafa ranar Laraba, Trump ya ce dandalin sada zumunta na kokarin dusashe ko kuma kashe kaifin muryar ma su ra'ayin rikau, a saboda haka za a rufesu ko kuma ake takaita tasirinsu.

"Jam'iyyar Republicans ta lura cewa dandalin sada zumunta na son kashe muryar ma su ra'ayin rikau. Za mu tashi tsaye wajen daidaita musu sahu, ko kuma mu rufesu, kafin su cimma muradinsu.

"Mun ga abinda su ka yi kokarin yi a 2016, amma ba su samu nasara ba. Ba zamu bari sabon sharrinsu ya yi tasiri a wannan karon ba," a cewar Trump.

Al'amuran siyasa na kara daukan zafi a Amurka a yayin da ake shirin sake gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 3 ga watan Nuwamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel