Amnesty ta bukaci a saki dan jaridar da ya soki Lai Mohammed

Amnesty ta bukaci a saki dan jaridar da ya soki Lai Mohammed

Kungiyar kare hakkin bil Adama, Amnesty International, ta bukaci rundunar 'yan sandan Najeriya ta gaggauta sakin wani dan jarida da ta kama, Rotimi Jolayemi, saboda ya soki ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed.

A rahoton da jaridar The Punch ta ruwaito, Amnesty ta bukaci a saki dan jaridar wanda a yanzu ya shafe tsawon makonni uku tsare a hannu hukuma saboda kawai ya soki Ministan na Najeriya.

Jolayemi wanda ya jagoranci wani shiri mai taken ‘Bi aye se ri’ da aka yada cikin harshen Yarbanci, ya fada hannun jami’an tsaro ne bayan ya rera wani wake wanda ya soki ministan labarai da al'adun kasar.

Dan jaridar ya shiga hannun jami'an tsaro na 'yan sanda a ranar 5 ga watan Mayu, biyo bayan yada wannan wake a gidajen rediyo na jihar Osun da Kwara wanda bai yi wa ministan kasar dadi ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, jami'an tsaro sun cafke matar Jolayemi da kuma 'yan uwansa maza biyu inda suka shafe tsawon mako guda a daure yayin da suka gaza bayyana inda dan jaridar ya ke.

Lai Mohammed, Jolayemi da matarsa
Hakkin mallakar hoto: Jaridar The Punch
Lai Mohammed, Jolayemi da matarsa Hakkin mallakar hoto: Jaridar The Punch
Asali: Twitter

Daga bisani an bari sun shaki iskar 'yanci bayan da Jolayemi ya mika kansa ga jami'an tsaro.

Jolayemi wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar 'yan jarida masu cin gashin kansu a Najeriya reshen jihar Osun, an garzaya da shi Abuja a ranar 7 ga watan Mayu inda aka ci gaba da tsare shi.

KARANTA KUMA: Dokar cin-gashin-kan majalisar jihohi da bangaren shari’a: Gwamnonin Najeriya za su gana ranar Laraba

Da ta ke martani dangane da wannan keta haddin bil Adama, kungiyar Amnesty cikin wani sako da ta wallafa a ranar Talata kan shafinta na Twitter, ta ce cafke dan jaridar da matarsa ya saba wa shari'a.

A sakon da Amnesty ta wallafa ta bayyana cewa: "Sabawa doka aka yi dangane da damkar Jolayemi da aka yi a ranar 6 ga watan Mayu, saboda wani wake da ya rera mai suka ga Ministan Labarai, Lai Mohammed."

"Haka zalika matarsa da aka kama kuma aka gallaza mata na tsawon kwanaki 8 ya sabawa tanadi na shari'a. Da wannan muke kiran jami'an tsaro su gaggauta sakin sa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng