Gwamnatin jihar Kano ta yi zazzafan martani a kan bidiyon cibiyar killacewa da ke yawo
- Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ce bidiyon da ke yawo na filin wasa na Sani Abacha da aka mayar da shi cibiyar killacewa a kofar mata duk yunkuri ne na bata sunan ayyukan da ake
- Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, yace babu wata alamar gaskiya a faifan bidiyon da aka fitar
- Garba ya ce an kara sauya fasalin cibiyar killacewar ne tare da gyara shi
Gwamnatin jihar Kano ta ce bidiyon da ke yawo na filin wasa na Sani Abacha da aka mayar da shi cibiyar killacewa a kofar mata duk yunkuri ne na bata sunan ayyukan da ake.
A wata takarda daga kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, yace babu wata alamar gaskiya a faifan bidiyon da aka fitar.
Kamar yadda yace, "Duk wanda ya fitar da wannan faifan ya lalata shi duk da kuwa ana kan aiki ne. Ya yi hakan ne don cimma wata manufa."
Malam Garba yace cibiyar killacewa ta Sani Abacha, wacce aka yi don gadaje 500 an kara sauya fasalinsa tare da gyara shi daga kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar shugaban kasa.
Ya ce a yayin da aka sake duba aikin, an cire gadaje 218 daga cikin 500 din da za a saka da farko zuwa wasu cibiyoyin killacewar.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa a halin yanzu cibiyar killacewa ta Sani Abacha na da gadaje 213 kuma cibiyoyin kiwon lafiya da suka kamata duk sun aminta da shi.
A gefe guda mun ji cewa gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta musanta rade-radin da ake yi na cewa ta yi watsi da kayan tallafin da gwamnatin tarayya ta ba jihar har ruwan sama ya lalata.
Kamar yadda kwamishinan watsa labarai na jihar, Muhammad Garba, ya aika wa manema labarai a yau Talata, ya ce ba gaskiya bane zargin. Ya ce kayan na nan babu abinda ya lalace sakamakon dukan ruwan saman.
Kwamishinan ya kara da cewa, tun kafin a kawo tallafin, ruwan sama ya dade da sauka a Kano kuma gwamnatin ta dauka matakin rufe hatsin da tamfol don hana su lalacewa.
Kamar yadda yace, kwamitin da aka dora wa alhakin tattara tallafin cutar korona din ya fara shirin rarraba kayan abinci ga talakawan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng