Saudiyya ta kawo karshen dokar kulle, ta sanar da lokacin bude Masallatai

Saudiyya ta kawo karshen dokar kulle, ta sanar da lokacin bude Masallatai

Saudiyya ta sanar da cewa za ta janye dokar kulle kulle kasar daga ranar 21 ga watan Yuni, amma banda a birnin Makkah, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta sanar ranar Talata.

An shafe fiye da watanni biyu da saka dokar kulle mai tsananin gaske a kasar Saudiyya domin dakile yaduwar annobar cutar korona.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiyya ya ce za a bude Masallatan da ke wajen birnin Makkah daga ranar 31 ga watan Mayu, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta sanar a jerin sakonnin da ta saki.

Kasar Saudiyya ta tsaurara dokar kulle kasar yayin bikin Sallar Eid el-Fitr da ake yi bayan kammala azumin watan Ramadana.

Annobar korona ta yi karfi sosai a kasar Saudiyya idan aka kwatanta da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.

Ma'aikatar ta ce za ta fara sassauta dokar kulle kasar daga satin nan da mu ke ciki ta hanyar fara sassauta dokar zaman gida daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 3:00 na ranakun Alhamis da Juma'a.

Za a kara sassauta dokar zuwa karfe 8:00 na dare daga ranar 20 ga watan Yuni, kamar yadda ma'aikatar ta sanar.

Saudiyya ta kawo karshen dokar kulle, ta sanar da lokacin bude Masallatai
Saudiyya za ta kawo karshen dokar kulle, ta sanar da lokacin bude Masallatai
Asali: UGC

Kasar Saudiyya za ta janye dokar kulle gaba daya daga ranar 21 ga watan Yuni.

"Daga ranar Alhamis, kasar Saudiyya za ta fara kaddamar da jerin matakan sassauta dokar kulle domin dawowar harkokin rayuwa kamar yadda aka saba duk da za a cigaba da aiki da dokar nesanta," a cewar Tawfiq Al-Rabiah, ministan lafiya na kasar Saudiyya.

DUBA WANNAN: An gano abinda ya haddasa barkewar Cacar baki tsakanin Pantami da hukumar NIDCOM

Sauddiyya ta sanar da cewa annobar korona ta kashe mutane 400 daga cikin jimillar mutane 75,000 da aka tabbatar da cewa kwayar cutar ta harba.

Tun a cikin watan Maris kasar Saudiyya ta sanar da dakatar da ziyarar Umrah domin gudun yaduwar cutar korona a birnin Makkah da Madinah.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce har yanzu dakatarwar na nan daram.

Hukumar kasar ba ta sanar da cewar ko za ta cigaba da shirin gudanar da aikin Hajji na wannan shekarar ba, wanda aka saba yi a cikin watan Yuli.

A kwanakin baya, mahukunta a kasar sun bukaci Musulmai su dakatar da shirin aikin Hajjin bana na wucin gadi.

Kimanin mutane miliyan 2.5 ne su ka ziyarci kasar Saudiyya a shekarar da ta gabata domin gudanar da aikin Hajji, wanda ake bukatar duk wani Musulmi da ke da hali ya gudanar ko da sau daya ne a rayuwarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng