Allah Sarki: Babbar Kanwar Uba na ta rasu a Gombe – Isa Ali Pantami

Allah Sarki: Babbar Kanwar Uba na ta rasu a Gombe – Isa Ali Pantami

- ‘Yaruwar Mahaifin Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ta rasu ana gama azumi

- Ministan kasar ya ce wannan Marigayiya, kanwa ce wurin Mahaifinsa

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin Najeriya, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya rasa wata goggorsa jim kadan bayan an kammala azumin watan jiya na Ramadan.

Mai girma ministan kasar ne ya bada sanarwar wannan babban rashi da ya yi ne da kansa a shafinsa na sadarwa na tuwita a jiya ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, 2020.

Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya rubuta: “Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Rajiun! Goggo na, mai bi wa Mahaifina ta rasu a yau (Ranar Litinin) a Gombe.” a shafinsa @DrIsaPantami.

Shararren malamin addinin kuma ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara da addu’a cewa: “Allah Ubangiji ya gafarta mata, ya kuma yi mata rahama.”

Legit.ng Hausa ta na da labarin cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya rasa mahaifinsa Ali Ibrahim Pantami da mahaifiyarsa Hajiya Amina Umar Aliyu tun shekarun baya.

KU KARANTA: Abin ya haddasa rigimar Minista Isa Pantami da Abike - Dabiri

A cewar ministan, wannan goggor ta sa da ta rasu, ita ce babbar kanwar mahaifinsa Ali Ibrahim Pantami. Jama’a da-dama sun aikawa Isa Pantami sakon ta’aziyyarsu.

Daga cikin wadanda su ka fara yi wa ministan sadarwar ta’aziyyar rashin da ya yi akwai Inuwa Kashifu wanda shi ne ya gaji Dr. Isa Pantami a kujerar hukumar NITDA.

Malam Inuwa Kashifu ya yi wa wannan Baiwar Allah addu’ar samun gafarar Ubangiji, sannan ya yi kira ga mai gidan na sa ya jure rashin da ya yi domin ya samu lada.

Idan ba za ku manta ba a watan Oktoban 2019 ne Dr. Isa Ali-Pantami mai shekaru 47 ya rasa wani yayansa, Is’haq, bayan watanni bakwai, sai kuma goggonsa ta biyo baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel