Za a rika bude kasuwannin Garin Abuja sau uku a mako duk da Coronavirus

Za a rika bude kasuwannin Garin Abuja sau uku a mako duk da Coronavirus

- Za a koma bude kasuwannin da ke Abuja har sau uku cikin kowane mako

- A baya kasuwanni su kan ci ne sau biyu kacal saboda annobar COVID-19

- Sakataren yada labarai na Ministan birnin tarayya ne ya bayyana wannan

Mun samu labari cewa mai girma ministan babban birnin tarayya, Muhammad Musa Bello ya kara yawan ranakun da za a rika bude kasuwannin Abuja daga kwanaki biyu zuwa uku.

Jaridar Punch ta ce an dauki wannan mataki ne bayan wani zama da aka yi tsakanin kwamitin da ke yaki da annobar COVID-19 a Abuja da kuma jami’an tsaro da ke birnin tarayyar.

An yi wannan zama ne a ranar Asabar, 21 ga watan Mayu, 2020 kamar yadda jaridar ta bayyana. Hukumomin su duba yiwuwar sassauta takunkumin da aka sa a birnin tarayyar kasar.

A wani jawabi da babban sakataren yada labarai na ministan ya fitar, za a koma bude kasuwanni da ke birnin Abuja yanzu a ranakun Litinin, Laraba da kuma Asabar na kowane mako.

KU KARANTA: An samu mutum 22 da COVID-19 ta harba a Garin Abuja - NCDC

Za a rika bude kasuwannin Garin Abuja sau uku a mako duk da Coronavirus
Wata Kasuwa a Najeriya. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kasuwannin za su rika ci ne tsakanin karfe 8:00 na safe da kuma 3:00 na yamma. Bayan haka kuma an bada damar a rika saida kayan noma kamar taki, iri, da magungunan kwari.

Za a dawo saida kayan wuta da na gine-gine a kasuwannin na Abuja da kewaye daga yanzu. Idan ba ku manta ba a kwanaki baya, kayan abinci kuruma aka halatta saidawa a kasuwanni.

“Kafin a bude duk sababbin sashen kasuwar kayan gini, sai an yi wa wurin tsaf. Ya zama dole ‘yan kasuwa su rika bin dokokin da aka sani na wanke hannu tare da kuma rufe fuskoki.”

FCTA ta kuma bada umarnin a guji shiga cikin cinkoso domin takaita yaduwar COVID-19. A halin yanzu wadanda su ka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya sun haura mutane 7, 500.

A karshe babban sakataren yada labaran Ministan ya ce: “Duk wasu matakai da hukumar FCTA ta kawo a ranar 2 ga watan Mayu, 2020 domin yaki da COVID-19 a birnin tarayya su na ci.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel