Yiwuwar ajiye azumi a Najeriya: An bukaci wadanda suka ga wata a jiya su bayyana kansu

Yiwuwar ajiye azumi a Najeriya: An bukaci wadanda suka ga wata a jiya su bayyana kansu

Rahoto ya nuna cewa biyo bayan sanarwa da Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad II ya fitar na tabbatar da daukar azumi a yau Asabar, 23 a watan Mayu, akwai yiwuwar sake duba batun ganin wata.

Kwamitin da ke kula da ganin wata a Najeriya wato ‘National Moon Sighting Committee’ ya fitar da sanarwar neman wadanda suka ga wata a jiya Juma’a, 22 ga watan Mayu, a fadin kasar.

Kwamitin wanda ya fitar da sanarwa a shafin Facebook yace dukkanin wanda ya san ya ga wata a fadin Najeriya to ya sanar da kwamitin saboda tattara bayanai domin mikawa mai alfarma Sarkin Musulmi.

“Dan Allah idan kana daga cikin wadanda suka ga jinjirin wata jiya Juma’a, 29 ga watan Ramadan 1441H (22 ga Mayu 2020) a fadin Najeriya, ko kuma ka san wanda ya tabbatar da ganin wata a jiya ko wasu mutane, tare da sanin yadda za a samu ayi magana da su, to ka tuntube mu.

“Mambobin kwamitin ganin wata zasu tuntube su domin su tattauna saboda suyi aikinsu wajen bayar da shawara ga mai alfarma Sarkin Musulmi don sauke hakki.

“Mun gode Jazakumullahu Khairan," in ji kwamitin.

A baya mun ji cewa majalisar Koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta sanar cewa za a cigaba da azumi a ranar Asabar.

Kwamitin duban wata ta NSCIA ta ce ba a ga wata ba a kasar saboda haka za a cigaba da azumi a ranar Jumaa.

Ta ce za a gudanar da azumi talatin a bana ba kamar yadda wasu musulmi suka fara shirin yin Idi a ranar Asabar ba.

Da ta ke sanar da sakamakon neman watar a ranar Jumaa, ta sanar da cewa "Ba a ga jaririyar watar Shawwal ba a Najeriya, gobe 30 ga watan Ramadan. Za a fitar da sanarwar daga ofishin sarkin musulmi nan ba da dadewa ba."

A wani labarin na daban, mun ji cewa a ranar Juma'a, 22 ga watan Mayu, mabiya Shi'a a Najeriya su ka gudanar da shagulgulan bikin Sallah bayan sun yi Sallar Idi.

KU KARANRA KUMA: Buhari ya haramta wa ministoci hukunta shugabannin cibiyoyi da ke karkashinsu

Sidi Manniru, shugaban mabiya Shi'a a jihar Sokoto, ya ce sun yi sallar Idi ranar Juma'a ne saboda sun ga jaririn watan Shawwal ranar Alhamis bayan sun yi azumi 29.

A hirarsa da wakilin jaridar Aminiya, Manniru ya ce mutanen da su ka yarda da su sun sanar da su cewa an ga jaririn watan Shawwal a garin Dukkuma a yankin karamar hukumar Isa da garuruwan Yabo da Illela dukkansu a jihar Sokoto.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel