'Yan bindiga sun kwace kauyuka a Sokoto, sun nada sabbin alkalai - Sanata Gobir
Dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin Sokoto na gabas a majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Gobir, ya yi ikirarin cewa 'yan bindiga sun kwace wani sashi na mazabarsa.
A wata tattaunawar da yayi da jaridar The Punch a Abuja ranar Juma'a, Gobir ya jajanta yadda 'yan ta'adda suka tsige sarakunan gargajiya da na siyasa a wasu kauyuka tare da nada nasu.
Kamar yadda dan majalisar APC din ya bayyana, wadanda kauyukansu ke da kusanci da iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar suna samun zaman lafiya saboda dakarun sojin kasar Nijar da ke basu kariya.
Dan majalisar yace, "Babban kalubalen da muke fuskanta a halin yanzu shine yadda 'yan bindiga ke kwace mana kauyuka da rana tsaka.
"Sun nada kansu a matsayin alkalai. Sun tsige sarakunan gargajiya da na siyasa, don haka su ke mulki.
"A halin yanzu 'yan bindigar ne ke sasanci a tsakanin jama'a idan an samu rashin jituwa. Su ke sasanta fada tsakanin mata da miji da sauransu."
Ya ce abinda ke faruwa a yankinsa ya zama wani abu daban saboda suna ta kira ga gwamnatin tarayya amma shiru kake ji.
Ya kara da cewa, "Idan aka duba halin da yankina yake ciki, babu noma saboda 'yan bindigar kashe jama'a suke yi idan suka gansu a gona.
DUBA WANNAN: Ba a ga wata ba a Najeriya, Idi sai ranar Lahadi –Sarkin Musulmi
Sanatan yace, "Idan ka siyar da Shanu, a daren ranar suke zuwa karbar kudin. Wani lokaci suna zagaye dukkan kauye ko gari sannan su kashe wanda suke so tare da diban abinda suke so, sai su kona sauran.
"Akwai lokacin da 'yan bindiga suka je yankinmu amma sai jama'a suka tsere zuwa daji. 'Yan bindigar sun bi su, inda suka kashe iyakar iyawarsu tare da bankawa dajin wuta."
Ya bayyana cewa sun dogara da dakarun sojin jamhuriyar Nijar ne.
Ya kara da cewa, "Su ke taimaka mana saboda suna kusa da iyaokin da ke makwabtaka da kauyukanmu. Da su yanzu muka dogara.
"Sojin Najeriya basu taimaka mana. Muna fuskantar kalubale mai tarin yawa a yankinmu. Idan muka kira dakarun sojin Najeriya, suna zuwa amma basu bin 'yan bindigar.
"Suna korafin cewa makaman 'yan bindigar sun fi nasu hatsari. Muna tattaunawa amma har yanzu babu wani ci gaba dake zuwa mana."
Gobir, wanda kokarinsa yasa aka hada jihar Sokoto cikin jihohin da za a tura dakaru don kawo karshen ta'addanci, ya yi tantamar kawo karshen lamarin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng