Hotunan yadda El-Rufa'i ya kafa ya tsare a kan iyaka don hana Kanawa shiga Kaduna

Hotunan yadda El-Rufa'i ya kafa ya tsare a kan iyaka don hana Kanawa shiga Kaduna

A yau, Juma'a, ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya jagoranci tawagar jami'an gwamnatinsa domin tabbatar da dokar hana shige da fice a tsakanin jihohi.

Jama'a da dama kan yi bulaguro a ranar jajiberin Sallah domin gudanar da shagulgulan bikin Sallah tare da iyalansu.

El-Rufa'i ya jagoranci jami'an gwamnatin ne zuwa kan iyakar jihar Kano da Kaduna domin tabbatar da cewa matafiya daga Kano ba su shiga yankin jihar Kaduna ba.

A hotunan da ya wallafa ashafinsa na tuwita, El-Rufa'i ya ce ya fita faturu iyakar ne domin ganin yadda ake yi wa dokar hana shige da fice biyayya.

Hotunan yadda El-Rufa'i ya kafa ya tsare a kan iyaka don hana Kanawa shiga Kaduna
El-Rufa'i yayin faturu a kan iyakar Kano da Kaduna
Asali: Twitter

El-Rufa'i ya kafa ya tsare a kan iyaka don hana Kanawa shiga Kaduna
Asali: Twitter

Hotunan yadda El-Rufa'i ya kafa ya tsare a kan iyaka don hana Kanawa shiga Kaduna
El-Rufa'i ya kafa ya tsare a kan iyaka don hana Kanawa shiga Kaduna
Asali: Twitter

A farkon makon nan ne gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce shi da kansa zai fita domin tsare iyakokin Kaduna da jihar Kano a ranar Sallah domin tabbatar da cewa babu wani da ya shigo jiharsa daga Kano a yunkurinsa na dakile yaduwar cutar.

Ana sa ran za a gudanar da bikin sallar na wannan shekarar a ranar Asabar ko Lahadi ne idan azumin watan Ramadan ya zo karshe.

DUBA WANNAN: 'Ku taimaka ku sakeni, lafiyata kalau' - Bidiyon mai jinyar korona tana rokon NCDC

El Rufai ya yi wannan gargadin ne a yayin hira da aka yi da shi a wasu gidajen rediyo a ranar Talata inda ya ce; "Da kai na zan fita in rika zaga iyakokin Kaduna da Kano kuma ba zan bar wurin ba sai dare don in ga wanda zai shigo Kaduna. Ba zan bar wurin ba sai dare."

Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda mutane ke shiga da fita jihar duk da umurnin shugaban kasa na hana zirga zirga tsakanin jihohi, inda ya ce galibin wadanda suke dauke da cutar a jihar sunyi tafiya.

Ya jingina laifi a kan wasu jami'an tsaro marasa kishin kasa da ke karbar cin hanci a hannun matafiya su barsu su shigo jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

El Rufai ya ce, "Ba abinda ba mu yi ba amma jamian tsaro ba su bamu hadin kai. Mun samu labarin yadda wasu direbobin motocin haya da wasu ke biyansu kudi don su shigo Kaduna."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel